in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi game da yaki da cutar tarin fuka
2018-09-28 16:14:32 cri
Jaridar The Guardian ta Nijeriya, ta ruwaito cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya gabatar da jawabi a wani taro mai muhimmanci na babban taron MDD karo na 73, inda ya bayyana cewa, cutar tarin fuka ta zama kalubalen da duk duniya ke fuskanta, kuma ya kamata kasashe daban daban su yi kokari tare don nazarin allurar rigakafi da magunguna don shawo kan cutar. Ya kuma ce, tun daga shekarar 2015, gwamnatin Najeriya ke kara bayar da kudi ga hukumomin kiwon lafiya, kana ta yi alkawarin za ta yi aikin gano cutar kyauta, ga mutane kimanin miliyan 40 a shekaru hudu masu zuwa, da nufin yin rigakafi da shawo kan cutar cikin lokaci. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China