in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS
2018-09-28 11:04:38 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da ya gudana jiya Alhamis a Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Wang Yi ya bayyana cewa, a watanni biyu da suka gabata, an yi ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin na Johannesburg, inda suka bayyana imaninsu na hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare.

Ya ce a mataki na gaba, ya kamata kasashen BRICS su kara yin hadin gwiwa a fannoni hudu. Na farko, ci gaba da tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban, da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da raya sabuwar dangantakar tsakanin kasa da kasa bisa girmama juna da tabbatar da adalci da hadin gwiwa da samun moriyar juna. Na biyu, a ci gaba da sa kaimi ga warware matsaloli ta hanyar shawarwari, da gabatar da ra'ayi iri daya kan manyan batutuwan duniya. Na uku, a ci gaba da yin kokarin samun bunkasuwa tare, da yin hadin gwiwa wajen tinkarar kalubale, da tabbatar da hakkin bunkasuwar sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban kasuwanci ciki har da kasashen BRICS. Na hudu kuma, a ci gaba da kara hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, da fadada tsarin hadin gwiwa na BRICS plus, don kafa dandalin hadin gwiwa mai muhimmanci a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China