in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya na ganawa da shugabannin 'yan kwadago game da yajin aiki
2018-09-28 13:49:03 cri

Yanzu haka dai ma'aika sun tsunduma yajin aiki na gama gari, a daukacin sassan tarayyar Najeriya, bayan da gwamnati da jagororin 'yan kungiyoyin kwadagon kasar suka gaza cimma matsaya, kan batun karin mafi karancin albashi ga ma'aikata. Sassan biyu dai sun tashi daga tattaunawar su ta daren jiya Alhamis ba tare da cimma matsaya ba. Tuni kuma kungiyoyin gwadagon kasar suka umarci ma'aikata da suka ci gaba da kauracewa wuraren ayyukan su har sai baba ta gani.

Kafin fara yajin aikin dai, sai da kungiyoyin kwadagon kasar suka baiwa gwamnatin tarayyar Najeriyar wa'adin makwanni biyu, na ta bayyana matsayar ta game da karin albashin da tuni aka dade ana tattaunawa a kan sa.

Yanzu haka dai gine ginen gwamnati a wasu jihohi na garkame, inda rahotanni ke cewa a Abuja fadar gwamnatin kasar, mafi yawa daga ofisoshin gwamnati suna rufe. Wakilan kamfanin dillancin labarai na Xinhua sun rawaito cewa, jagororin kungiyoyin 'yan kwadagon na kewayawa, domin tabbatar da ba wani ma'aikaci da ya halarci wurin aikin sa.

Wasu rahotannin na cewa, an daga turar kungiyar kwadago ta NLC, a gaban babbar kofar shiga ma'aikatar kudin Najeriya, a wani mataki na nuna jajircewar kungiyar ta NLC game da yajin aikin. Kaza lika an kafa wata turar kungiyar a gaban ginin ma'aikatar lafiya.

Tsagin gwamnatin tarayyar kasar dai ya tabbatar da cewa, ba a kai ga cimma matsaya ba, a zaman da ya yi da shugabannin 'yan kwadagon kasar a daren ranar Alhamis. Bankuna da makarantu, na cikin sassan da suka shiga yajin aikin a wasu bangarorin kasar, ciki hadda birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, ko da yake a jihohi da dama ma'aikata na ci gaba da zuwa wuraren aiki.

Wasu mutane da suka zanta da kamfanin daillancin labarai na Xinhua sun bayyana cewa, bankuna sun rufe kofofin su, don haka ba su da damar gudanar da hada hadar kudade da suka saba yi yau da kullum a bankunan.

A daya hannun kuma, filin jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja na bude, jirage suna kuma ci gaba da zirga zirgar kamar yadda aka saba, kamar dai yadda wakilan Xinhua suka tabbatar. Sai dai wani jami'in kungiyar ma'aikatan filayen jiragen saman ya shaidawa Xinhua cewa, kungiyar su na goyon bayan kungiyar kwadago ta NLC, illa dai kawai jagororin su na halartar wani taro a kudancin kasar, hakan ne kuma ya sa, ba su matsa lamba wajen tabbatar da an aiwatar da matakin yajin aikin ba tukuna.

A filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed dake birnin Ikkon Jihar Lagos ma, mambobin kungiyar NLC sun rufe ofisoshin hukumar gudanarwar sa, amma hakan bai shafi zirga zirgar jama'a, da tashin jiragen sama yadda aka saba ba.

Duk da cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya na fatan yajin aikin da aka fara zai karade dukkanin sassan kasar, a jihohi da dama cikin hadda Kaduna da Yobe, ma'aikata na ci gaba da zuwa ofisoshin su.

Ko da ma a birnin tarayya Abuja, wasu makarantu, da Asibitoci da babban bankin kasar CBN, da ofisoshin kamfanoni masu zaman kan su, na ci gaba da aiki kamar yadda suka saba.

Da yake karin haske game da yadda taro tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan kwadago ya wakana, ministan ma'ikatar kwadago da nagartar aiki Chris Ngige, ya ce tattaunawar ta yi armashi. Ya ce sun yi shawarwari da tsagin 'yan kwadagon, wadanda ke matsayin daya daga bangarorin kwamitoci 3, masu ruwa da tsaki game da batun karin albashin.

Mr. Ngige, ya ce ya gabatarwa sassan masu ruwa da tsakin matsayar gwamnati game da wannan batu, kana dukkanin sassan sun amince a koma teburin shawarwari, karkashin lemar kwamitin neman karin albashi, a ranar 4 ga watan Oktoba mai zuwa. Ya ce hakan zai ba hukumar tsara albashi ta kasa dama, ta kammala ayyukan ta masu nasaba da wannan batun karin albashin.

Jagororin kungiyoyin kwadago a Najeriyar dai na son matsawa gwamnatin kasar, ta fara biyan sabon tsarin albashi, sama da mafi karanci da ake biya yanzu wato Naira 18,000, kimanin dalar Amurka 50, zuwa Naira 56,000, suna masu cewa tsarin albashin na yanzu ya sabawa hakikanin halin da 'yan kasar ke ciki, musamman idan aka yi duba da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi.

An dai amince da biyan mafi karancin albashi na Naira 18,000 ne, lokacin da ake musayar kudin kasar kan Naira 145 kan kowace dalar Amurka shekaru sama da 8 da suka gabata. Sai dai yanzu dalar ta Amurka ta kai Naira kusan 360 a kasuwannin bayan fage.

Tun a ranar 12 ga watan Satumbar da ta gabata ne, kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka yi kashedin cewa, sun lura gwamnati na jan kafa, game da bukatar su ta neman karin albashin, inda suka yi kira ga kwamitoci 3 da aka dorawa nauyin nazartar wannan batu, su kammala ayyukan su kan lokaci, ko a kaucewa fadawa yajin aiki.

Idan dai ba a manta ba, a watan Nuwambar shekarar bara, shugaban Najeriya Muhammdu Buhari, ya kaddamar da kwamitoci 3 masu mambobi 30, wadanda aka dorawa nauyin tattaunawa game da batun karin albashin. Kwamitocin sun kunshi wakilan ma'aikata, da na kamfanonin dake daukar ma'aikata, da walikan gwamnatocin tarayya da na jihohin kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China