Shugaba Faustin-Archange Touadera ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yana mai cewa kudurorin wadanda suka hada da bunkasa raya masana'antu, da samar da manyan ababen more rayuwa, da bunkasa cinikayya da zuba jari ba tare da gurbata muhalli ba, na da matukar muhimmanci. Shugaban ya ce yana matukar sha'awar yadda Sin ke ba da tallafin kwarewa ga kasashen Afirka.
Ya kara da cewa, idan ana son gina kasa, dole ne a fara da samar da horo na kwarewar aiki. A wannan fanni kasar Sin ta taimakawa Afirka da dabarun sanin makamar aiki. Hakan a cewar sa mataki ne da ya dace matasan nahiyar su yi na'am da shi.
Game da tasirin bashin Sin ga kasashen Afirka kuwa, Mr. Touadera ya ce nahiyar na bukatar kudaden gina ababen more rayuwa, duba da cewa idan ba bu kudade, zai yi wuya kasashe kamar jamhuriyar Afirka ta tsakiya su samu damar bunkasuwa. Don haka a cewar sa bashin da Sin ke samarwa muhimmin taimako ne ga kasashen nahiyar. (Saminu Hassan)