in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana Kokarin Kafa Sabuwar Kafar Yada Labarai Da Babu Irinta A Duniya
2018-09-26 22:05:50 cri
A yayin da gidan talibijin na kasar Sin, wato CCTV ke cika shekaru 60 da kafuwa da kuma cika shekaru 60 da fara sha'anin talibijin bayan kafa sabuwar kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya nuna yabo sosai kan manyan nasarorin da aka cimma wajen ci gaban aikin talibijin na kasar, ya kuma ba da tabbaci kan bunkasuwa da nasarori da aka samu bayan kafuwar babbar hukumar gidan Rediyo da Talibijin ta kasar Sin wato CMG a takaice, kana ya gabatar da sabbin bukatu game da bude sabon babi na yayata aikin talibijin na kasar Sin.

A cikin shekaru 60 da suka gabata, a matsayinsa na ginshiki a fannin aikin talibijin, ko da yaushe CCTV na tsayawa kan yin kwaskwarima da yin kirkire-kirkire, hakan ya taimaka wajen raya aikin talibijiin da na watsa labaru sosai. Ma'aikatan talibijin na kasar Sin na alfahari da nasarorin da aka samu a fannin aikin talibijin a cikin shekaru 60 da suka gabata.

Shugaba Xi ya bukaci da a kafa sabuwar kafar watsa labaru da ta dara kowace a duniya a fannin karfi na jagoranci, yada labaru da kuma tasiri. A watan Maris din bana ne, aka kafa hukumar CMG, matakin da ya kai ga samar da dandamali mai kyau domin cimma wannan buri.

A matsayinta na babbar hukumar kula da kafofin talabijin da rediyo mallakin gwamnatin kasar Sin, ya kamata hukumar CMG ta tsaya tsayin daka kan jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da watsa labarai bisa manufofin jam'iyyar, da bayyana ainihin ma'anar tunanin Xi Jinping na tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin na sabon zamani, da himmatuwa kwazo wajen fadakar da jama'a kan tunanin yin kirkire-kirkire na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Babbar hukumar kula da kafofin talabijin da rediyo ta kasar Sin wato CMG a takaice da aka kafa, ta shata alkiblar harkokin watsa labarai ta kafofin talabijin da rediyo na kasar Sin baki daya. Ya kamata hukumar CMG ta ba da muhimmanci ga muradun jama'a, da aiwatar da babban nauyin da ya rataya a wuyanta, da kuma bunkasa kafofin watsa labarai na gargajiya da na zamani tare, da amfani da kwarewarta wajen watsa labarai zuwa kasashen waje, da nuna azama wajen yin kwaskwarima da gyare-gyare, a wani mataki na cimma burin kafa sabuwar babbar kafar watsa labarai ta kasa da kasa dake da babban tasiri da karfi wajen watsa labarai. (Masu Fassarawa: Bilkisu Xin, Murtala Zhang, ma'aikatan Sashen Hausa)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China