Hukumar raya ilimi, kimiya da al'adu ta MDD(UNESCO) ta yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su kara daukar matakan ingangta ilimin yara mata a duniya, don ganin ba a bar kowa ce 'ya mace a baya ba.
Bugu da kari, hukumar ta UNESCO ta bukaci al'ummomin kasashen duniya da su yi kokarin cimma muradun samar da ilimi kyauta kuma mai inganci na tsawon shekaru 12 ga dukkan yara maza da mata nan da shekarar 2030, da bullo da dokoki a dukkan kasashe don ba da tabbaci ga 'yancin samar da ilimi.
Alkaluman hukumar na nuna cewa, kimanin yara mata miliyan 132 ne ba sa zuwa makaranta. (Ibrahim)