in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kwadago a Nijeriya ta kira yajin aiki game da mafi karancin albashi
2018-09-26 09:45:47 cri

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya za ta fara yajin aiki a gobe Alhamis, domin nuna rashin amincewarta da gazawar gwamnatin kasar na mayar da martani game da wa'adin kwanaki 14 da ta bata na fara biyan mafi karancin albashi.

Wata sanarwa da Musa Lawal Ozigi, Sakatare Janar na hadaddiyar kungiyar ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu TUC ya fitar, ta ce an cimma matakin ne yayin taron kwamitin gudanarwa na kungiyar da ya gudana a ranar Litinin, a don haka, aka ayyana tsunduma yajin aiki daga sanyin safiyar gobe Alhamis 27 ga wata.

A cewa Musa Ozigi, ana jan hankalin dukkan ma'aikata da kungiyoyin al'umma da sauran jama'ar kasar da su tanadi dukkan kayayyakin masurufi da za su bukata.

Ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar da su tsumayi karin umarnin daga kungiyar kafin ko ranar Alhamis. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China