Paul Njuguna, kakakin rundunar tsaro ta KDF, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an yi mummunan gumurzu tsakanin dakarun tsaron da mayakan al-Shabab inda dakarun na Kenya suka samu nasarar hallaka mayakan a arewacin Pandaguo dake shiyyar Lamu na kasar Kenya.
Bayan hallakan mayakan na Alshabaab 10, sojojin sun kuma gano bindigogi kirar AK47 guda 7, da alburusai. Sojojin suna ci gaba da farautar sauran mayakan da suka tsere da raunuka a jikinsu, in ji jami'in. (Ahmad Fagam)