in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya za su kare matsayin gamayyar kasa da kasa
2018-09-25 10:32:14 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Birtaniya Jeremy Hunt, sun sha alwashin kare matsayin tsarin kasa da kasa da ake amfani da shi a halin yanzu da kuma gamayyar kasa da kasa a daidai lokacin da ake fuskantar kalubaloli.

A lokacin ganawarsu a gefen babban taron MDD, Wang ya ce, kasar Sin da Birtaniya dukanninsu mambobi ne masu kujerun dindindin a kwamitin tsaron MDD, akwai bukatar su kara daidaita dangantakar dake tsakaninsu a yayin da ake fama da fargaba da rashin tabbatar a harkokin kasa da kasa.

Kasar Sin ta nanata matsayinta na yin hadin gwiwar moriyar juna da samun ci gaba tare, kuma ba za ta taba bin tsohon salon da yammacin duniya ke amfani da shi ba na nuna karfin tuwo da yin babakere ga kasashen duniya ba, in ji mista Wang.

Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka zama tushe kuma kasar dake taimakawa tsare tsaren tafiyar da harkokin kasa da kasa dake gudana a halin yanzu, in ji Wang, ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta karfafa hadin gwiwarta da sauran kasashen duniya ciki har da Birtaniya domin kare muradun gamayyar kasa da kasa da kuma warware dukkan nau'ikan kalubaloli.

A nasa bangaren, Hunt ya ce, Birtaniya tana matukar martaba dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma a shirye take ta gina kyakkyawar alaka a sabon karni tare da kasar Sin.

Birtaniya ba ta daukar kasar Sin a matsayin barazana, kuma a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin wajen kiyaye dokokin kasa da kasa da kara zurfafa tattaunawa da yin musaya da hadin gwiwa daga dukkan fannoni tare da kasar Sin, in ji Hunt. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China