Ginin kogon layin dogon dai na da tsawon kilomita 4.5, kuma bangare ne na zangon aiki mai lamba 2A, mai kunshe da cikakken layin dogo ko "Standard Gauge" a Turance.
Da yake karin haske game da nasarar da aka samu a aikin na ginin kogon layin dogon Ngong, babban manajan CCCC mai lura da aikin An Aijun, ya ce kamfaninsa ya shawo kan kalubalen da ya fuskanta yayin aikin ginin, wanda hakan ke nufin za a kai ga kaddamar da aikin bayan kammalar sa a cikin shekara mai zuwa.
An Aijun ya ce kamfanin zai kare muhalli, da kare ka'idojin aikin, zai kuma ci gaba da baiwa al'ummun da aikin ya shafa tallafin kyautata zamantakewar su.
A nasa tsokaci, shugaban kamfanin jiragen kasa na kasar Kenya Michael Waweru, ya ce aikin layin dogon da ya ratsa duwatsu na cikin muhimmin ci gaba da harkar sufurin jiragen kasan kasar Kenya ya samu. Ya ce hakan na shaida yadda gwamnatin kasar Kenya ke daukar matakan zamanantar da ababen more rayuwa, da inganta zamantakewar al'umma yadda ya kamata. (Saminu Hassan)