in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar Bayani Ta Nuna Hakikanin Shaidu Da Matsayin Gwamnatin Kasar Sin Kan Takaddamar Cinikayya Dake Tsakaninta Da Amurka
2018-09-24 20:15:56 cri

Yau Litinin 24 ga wata, rana ce ta bikin tsakiyar yanayin kaka wato Mid-Autumn Day ga al'ummar kasar Sin. A ranar ce kuma, Sin ta fitar da takardar bayani game da shaidu da matsayinta kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka, inda ta yi bayani filla-filla kan hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da cinikayya dake kawowa juna moriya, da karyata zargi maras tushen da Amurka ta yiwa kasar Sin a cikin rahoton bincikenta mai lamba 301, tare kuma da bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin dangane da takaddamar cinikayyar dake tsakaninta da Amurka.

Gwamnatin Amurka ta yi biris da ra'ayoyin jama'ar duniya inda ta ci gaba da tsananta yakin cinikayya da kasar Sin, al'amarin da ya kara kawo illa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. A daidai wannan lokaci, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wannan takardar bayani, da bayyana hakikanin shaidu kan lamarin, matakai da zai iya taimakawa duniya kara fahimtar ainihin abubuwan da suka haddasa takaddamar cinikayyar Sin da Amurka, da kara fahimtar ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin dangane da samun fahimtar juna da inganta hadin-gwiwa tsakaninta da Amurka.

Takardar bayanin na kunshe da haruffan Sinanci 36000, inda aka zayyana dimbin alkaluma da misalai da sauransu, wadanda akasarinsu aka tsamo su daga hukumomin gwamnatin Amurka da manyan kamfanonin kasa da kasa da shahararrun cibiyoyin nazarin kasa da kasa gami da littattafan da shahararrun masana suka rubuta. A cikin wannan takardar bayani, ana iya ganin damuwa gami da ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da Amurka, da kuma matukar kokarin da Sin take yi wajen kiyaye moriyar bai daya ta Sin da Amurka gami da tsarin cinikayya na duk fadin duniya.

Takardar bayanin mai sassa shida ta yi bayanai kan fannoni guda uku:

Na farko, ta bayyana hakikanin shaidu da gaskiyar lamarin kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, da bayyana ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayin nuna fin karfinta da Amurka ke nunawa, gami da illolinsu.

Daya daga cikin hujjojin da Amurka ke fakewa da su wajen kaddamar da takaddamar cinikayya kan kasar Sin shi ne, wai kasar Sin ta fi Amurka cin moriya daga hadin-gwiwarta da Amurka ta fannin tattalin arziki da cinikayya, sabili da haka, Amurka ta bukaci da a gudanar da cinikayya "cikin adalci" da budewa juna kofa "daidai wa daida". Kalaman na kasar Amurka suna iya kawo rashin fahimta ga mutanen da ba su san hakikanin gaskiyar al'amarin ba. Takardar bayanin ta gabatar da kwararan shaidu daga bangarori daban-daban don nuna cewa, hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da cinikayya, hadin-gwiwa ce dake kawowa juna moriya, ba wai wani bangare ne kadai ya ke cin moriya ba,. Don haka, kalaman Amurka na cewa wai ta yi hasara, sam ba su da tushe balle makama. Har wa yau kuma, takardar bayanin ta gabatar da kwararan shaidu da dama don karyata wasu zarge-zargen da Amurka ta yiwa kasar Sin, ciki har da rashin daidaito tsakanin cinikayyar Sin da Amurka, da rashin adalci tsakanin cinikayyarsu, da satar 'yancin mallakar fasaha, da tilasta a yi musanyar fasahohi da manufar samar da tallafi ga masana'antu da sauransu.

Takardar bayanin ta nuna cewa, manufar samar da gajiya da moriyar juna da kungiyar WTO ta gabatar ta yi la'akari da bambancin matsayin ci gaba na kasashe daban daban, lallai ta tabbatar da adalci na ainihi a duniya. Amma, "gudanar da cinikayya cikin adalci" da "bude kofa cikin daidaito" da kasar Amurka ke magana a kai, sun saba bambancin dake tsakanin kasashe daban daban a fannonin matsayin ci gaba, da albarkatu, da fifikon masana'antu da dai sauransu, kuma sun kyale ikon ci gaba na kasashe masu tasowa, hakan ba shakka zai lalata rushe tattalin arziki da masana'antun kasashe masu tasowa, sannan zai kara haifar da rashin adalci.

Na biyu, takardar bayanin ta bayyana matsayin kasar Sin kan batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da Amurka da kuma alakar dake tsakanin kasa da kasa.

Tun bayan da kasar Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya kan kasar Sin a cikin rabin shekarar da ta gabata, kullum kasar Sin na tsaya kan matsayinta kan batun. Game da haka, takardar bayanin ta yi bayani a fannoni guda takwas, ciki har da matsayin kasar Sin game da kiyaye mutunci da muradunta, tsayawa kan ciyar da dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da Amurka gaba yadda ya kamata, tsayawa kan kiyaye da inganta tsarin cinikayya na bangarori da dama, tsayawa kan kiyaye 'yancin mallaka da 'yancin mallakar fasaha, tsayawa kan kiyaye 'yancin 'yan kasuwan kasashen waje dake kasar Sin, tsayawa kan zurfafa yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, tsayawa kan karfafa hadin kai irin na samun moriyar juna da samun nasara tare da sauran kasashe masu ci gaba da wadanda ke tasowa, tsayawa kan inganta kafuwar al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da dai sauransu. Ana iya fahimtar cewa, matsayin kasar Sin a fannonin nan guda takwas ba kawai ya yi la'akari da batun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka ba, har ma ya yi la'akari da yadda ake iya samun ci gaban alakar kasa da kasa yadda ya kamata, hakan ya nuna siffarta ta babbar kasa dake daukar nauyi kanta.

Na uku, takardar bayanin ta gabatar da hanyar da ta dace wajen warware takaddamar cinikayya a tsakanin Sin da Amurka.

Takardar bayanin na ganin cewa, matsayin ci gaba da ma tsarin tattalin arzikin kasashen biyu ya bambanta, don haka, ba wani abu ba ne idan aka samu takaddamar cinikayya daga lokaci zuwa lokaci. Amma, abu mai muhimmanci shi ne, yadda kasashen biyu za su karfafa amincewa da juna, da bunkasa alakarsu da ma yadda za su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Takardar bayanin ta nuna cewa, takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka na iya yin tasiri ga zaman lafiya da wadatuwar tattalin arzikin duniya, da kuma alaka da zaman lafiya da ci gaban duniya, ya kamata a warware matsalar yadda ya kamata. Takardar bayanin ta jaddada cewa, ko da yaushe kofar kasar Sin a bude take wajen yin shawarwari, amma dole ne a yi shawarwari bisa tushe na girmama juna, da daidai wa daida, da kuma cika alkawari.

Babu wanda zai ci nasara a yakin cinikayya. Idan ana son warware matsalar, wajibi ne a karanta wannan takardar bayani, don fahimtar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya irin na samun moriyar juna da samun nasara tare, kuma a yi la'akari da muradun jama'ar kasashen biyu, tare da sake komawa kan hanyar da ta dace wajen warware takaddamar cinikayya a tsakanin bangarorin biyu. (Murtala Zhang, Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China