in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa a wurare daban daban na murnar bikin tsakiyar yanayin kaka
2018-09-24 15:16:54 cri

Yau Litinin rana ce ta bikin tsakiyar yanayin kaka na gargajiyar kasar Sin. An shirya shagulgula na musamman don murnar bikin a wurare daban daban dake fadin kasar, ciki har da dafa wainar wata, wata irin wainar da ake yi da garin alkama da sukari da markadadden dabino da sauran abinci masu dadi da ake sakawa a ciki, da amsa tambayoyin wasan kwakwalwa da aka rubuta kan fitilu da dai sauransu, inda jama'a suke kara fahimtar bikin. Irin wadannan ayyuka su kan jawo hankulan mutane kwarai da gaske.

Ban da wannan kuma, akan rage farashin tikiti a wasu muhimman wuraren yawon shakatawa gabanin bikin, hakan ya sa Sinawa dake son zuwa yawon shakatawa a lokacin hutu na bikin suke cin gajiyar wannan dama.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China