in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya taya manoman kasar murnar bikin gurbe amfanin gona na farko
2018-09-23 20:05:01 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin dabarun kasar na farfado da yankunan karkarar kasar, matakin da shugaban ya bayyana a matsayin abin tarihi.

Shugaba Xi ya kuma yi kira da a rika bikin tunawa da ranar girben amfanin gona na manoma na farko a kasar Sin, bikin da ya fado a yau.

Yayin tunawa da bikin, shugaba Xi ya ce an cimma nasarori da yin gyare-gyare a bangaren aikin gona da raya yankunan karkara da tarihi ba zai taba mantawa da su ba a cikin shekaru arba'in da suka gabata da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare

Bugu da kari, ya yi kira da a kara daukar sabbin matakai don hade birane da yankunan karkaka da tsarin zamanantar da sassan biyu, da kara zage damtse wajen inganta jam'iyyun gama kai na manoma da gonakan iyalan domin kara inganta bangaren aikin gona.

Shugaba Xi ya kuma ba da shawarar kara samar da kudade a fannonin aikin gona da kayayyakin more rayuwar jama'a a yankunan karkarar kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China