in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a nuna wasan Cartoon na kasar Sin a gidajen sinima da dama a Najeriya
2018-09-23 16:56:06 cri
Za'a nuna wasan Cartoon na Sinawa a gidajen sinima masu yawa a Najeriya nan da karshen shekarar 2018.

Wasan kwaikwayon, mai taken, Travel with the Wind, wanda wani kamfanin shirya fina-finai na Hangzhou Minglang na kasar Sin ya shirya, ya bada labari mai karfafa gwiwa game da yadda wata karamar dabbar dinosaur mai suna 'Wind' ta fuskanci wahalhalu a kungurmin daji.

Ana saran zai iya sanya farin ciki ga iyalai a Najeriya, Rosana George, wata jami'ar kamfanin yada labarai na Silverbird, ta bayyana hakan ne a taron manema labarai a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Kamfanin Silverbird yayi hadin gwiwa tare da kamfanin Minglang na kasar Sin domin daga matsayin shirin Cartoon din na Sin a Africa, ta kara da cewa, shirin wasan zai kara kyautata dangantaka dake tsakanin kamfanonin kasashen biyu.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China