in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutane da suka mutu a hadarin jirgin ruwa a Tanzaniya ya kai 218
2018-09-23 16:21:34 cri
Kafefen yada labaran cikin gidan kasar Tanzaniya sun bada rahoto a jiya Asabar cewa adadin mutanen da suka hallaka a sanadiyyar kifewar jirgin ruwa a tekun Victoria ya karu zuwa 218.

Ministan ayyukan sufuri da sadarwa na kasar Isack Kamwelwe, ya ce ana cigaba da zakulo karin gawarwaki a yayin da masu aikin ceto ke cigaba da gudanar da ayyukansu.

Ya ce kayayyakin aikin da ake son yin amfani da su don tsamo wadanda ibtila'in ya afka musu suna kan hanyar zuwa tekun daga Mwanza, babbar tashar ruwa ta shiyyar arewa maso yammacin kasar.

A ranar Juma'a ne dai shugaban kasar Tanzanian Magufuli ya bada sanarwar ware kwanaki hudu a matsayin makomi don nuna juyayi ga wadanda hadarin ya rutsa da su.

A cewar majiyar, jirgin ruwan wanda ke da karfin daukar fasinjoji 101 da jiragen takon kaya masu nauyin ton 25, ya kife ne da misalin karfe 1 na yamma daidai da karfe 10 agogon GMT na ranar Alhamis.

Sakamakon bincike na farko ya nuna cewa, jirgin mallakin kasar an yi masa lodin da wuce karfin ikonsa, kuma wanda ke tuka jirgin bashi da kwarewar tuka jirgin ruwa mai dakon manyan akwatunan dakon kayayyaki. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China