in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An lalata sama da bindigogi da abubuwan fashewa 140,000 a kasar Sin
2018-09-23 16:08:44 cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, 'yan sandan kasar sun yi nasarar warware sama da kararraki 33,000 da suka shafi bindigogi da abubuwan fashewa, tun lokacin da aka kaddamar da yaki da miyagun laifuffuka a sassan kasar a watan Fabrairun wannan shekara.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce jami'an tsaro a kasar suka lalata sama da bindigogi 140,000 da tarin abubuwan fashewa dake hannun jama'a ba bisa ka'ida ba a birane 146 na kasar.

Bayanai na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Agustan wannan shekara adadin laifukan da ake aikata da bindigogi da abubuwan fashewa sun ragu daga kaso 36.1 cikin 100 zuwa kaso 30.5, bisa makamancin lokaci na bara.

Mataimakin ministan kula da harkokin tsaron jama'a Sun Lijun ya ce, shirin yaki kan masu aikata laifuffka da bindgogi da abubuwa fashewa da aka kaddamar a sassan kasar ya yi nasara, amma har yanzu akwai sauran kalubale.

Don haka, ya yi kira ga dukkan ofisoshin 'yan sanda dake kasar, da su kara dauka damar ganin bayan wadannan manyan laifuffuka.

A kasar Sin dai an haramta wa fararen hula mallakar bindigogi. Kuma kasar ta dade tana daukar matakan yaki da masu amfani da bindigogi da ababan fashewa suna aikata manyan laifuffuka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China