in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 44 ne suka mutu a Tanzaniya bayan da kwale-kwalen da suke cike ya nutse
2018-09-21 11:19:39 cri
Gwamnatin Tanzaniya ta sanar da cewa, a kalla mutane 44 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwalen fasinja da suke ciki ya nutse a tafkin Victoria.

Kwamishinan yankin Mwanza, John Mongela ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, an yi nasarar ceto mutane 37. Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike amma akwai fargabar adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

A cewar wasu majiyoyi, kwale-kwalen mai dauke da fasinjoji 101 da kayayyakin da suka kai nauyin tan 25 ya kifene da misalin karfe 1 na rana agogon yankin.

Kwamishinan 'yan sandan yankin Mwanza Jonathan Shana, ya ce tawagar masu aikin ceto na ci gaba da tsamo gawawwakin da suka bace. Tuni kuma aka mika wasu daga cikin gawawwakin da aka gano ga 'yan uwansu.

Har yanzu dai ba a san musabbanin kifewar kwale-kwalen ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China