in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya tattauna da wakilan dake halartar taron Davos
2018-09-21 10:09:59 cri
A jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tattauna da wakilai daga bangarorin masana'antu da kasuwanci da harkokin kudi da masu ruwa da tsaki da kafofin watsa labarai dake halartar taron dandalin tattalin arziki na duniya na Davos na wannan shekara dake gudana a birnin Tianjin dake nan kasar Sin.

Yayin ganawar da shugaban dandalin Klaus Scwab ya jagoranta, Firaminista Li ya amsa tambayoyin da aka gabatar masa game da manufar bude kofa kan harkokin kudi na kasar Sin da 'yancin kare mallakar fasaha, da haraji da rangwame biyan wasu kudade, da harkokin masana'antu da kirkire-kirkire da ma tsarin yiwa harkokin cinikayya na duniya gyaran fuska da sauransu.

A jawabinsa Li ya ce, kasarsa na daukar matakan bude kofa kan harkokin kudi bisa ga ci gaban da take samu, da matsayin tattalin arzikinta gami da karfin dokokin da ta shata.

Ya ce, kasar Sin tana kokarin daidaita harkokin kudi, da kara bude kofa ga hidimomin da suka shafi harkokin kudi, da baiwa kamfanoni da masu zuba jari na ketare dama kamar takwarorinsu na cikin gida da kawar da adadin ba da lasisin tafiyar da harkokin kasuwanci da mallakar kamfanonin katare.

Da ya juya ga batun tsarin yiwa harkokin cinikayya na duniya gyaran fuska kuwa, firaminista Li ya yi nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu, tsarin ba da kariya ga harkokin cinikayya yana kokarin girgiza ginshikin dokokin cinikayya tsakanin bangariri da dama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China