in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin tattaunawa kan hanyar siliki ta teku ta karnin 21 ya ba da damar waiwayen tarihi da ma hada kasashen duniya
2018-09-21 09:43:17 cri

Jiya ranar Alhamis, aka bude taro karo na biyu na dandalin tattaunawa kan harkokin watsa labaru na kasashen da ke kan hanyar siliki ta teku ta karnin 21 a birnin Zhuhai da ke kudancin kasar Sin, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da gwamnatin lardin Guangdong suka karbi bakuncin gudanar da shi. Taron ya samu halartar sanannun kwararru da masana da ma manyan jami'an kafofin watsa labarai, inda suka tattauna kan matakan da aka dauka da ma sakamakon da aka samu bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", gami da yadda za a inganta hadin gwiwa a tsakanin kafofin watsa labarai.

Shekarar bana wato ta 2018 shekara ce ta cika shekaru 5 da Shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", wadda ta kasance wani babban shiri mai matukar ma'ana da ya ratsa nahiyoyi da tekuna, da hada tarihi da makoma, da ma hada Sin da sauran kasashen duniya.

A cikin baki masu halartar taron dandalin tattaunawa kan hanyar siliki ta teku, akwai dimbin aminan jama'ar kasar Sin. Tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin yana daya daga cikinsu, wanda 'yan kasarsa ke kira Mista Sin. Mr. Raffarin ya nuna babban yabo ga shawarar "ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar. Har ma a bikin bazara na kasar Sin na bana, ya wallafa sako a shafinsa na sada zumunta cewa, yana fatan shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta zama sabuwar hanyar kyautata dankon zumunci a tsakanin Faransa da Sin. Yana mai cewa,

"Za mu inganta hadin kanmu a karkashin shirin 'zirin tattalin arziki da ke kan hanyar siliki', da na 'hanyar siliki ta teku ta karnin 21'. Hadin kanmu zai shafi fannonin raya muhimman ababen more rayuwa, da yin cinikayya, da zuba jari. Bisa wadannan shirye-shiryen biyu, dukkan kasashen da abin ya shafa za su tattauna sosai kan yadda za su raya makomarsu. Lallai wannan wani muhimmin batu ne ga Turai."

A yayin taron, Forfesa Thomas J.Sargent na Jami'ar New York, wanda ya taba lashe lambar yabo ta Nobel a fannin tattalin arziki a shekarar 2011 ya gabatar da wani jawabi mai taken "Sabon zamani, sabon salon tattalin arziki, sabbin fasahohi: shekaru 40 masu zuwa na lardin Guangdong", inda yake ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta dace da ci gaban sabon zamanin da muke ciki. Ya kara da cewa,

"Ba ma kawai shawarar 'ziri daya da hanya daya' za ta amfana wa kasar Sin ba, duniya baki daya ma za ta ci gajiyarta, ganin yadda ta kawo sabuwar takara, wadda za ta taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da ma fito da sabbin tunani a duk fadin duniya."

Bisa shirin da ya shafi hanyar siliki, za a cimma ra'ayi bai daya, da watsa tunani, da cudanyar al'adu, da ma kyautata zumunci. A nan gaba, ba za a iya raba jimlar "hadin kai" ba, ko a fannin cinikayya, ko a fannin al'adu, ko ma a fannin kafofin watsa labarai. Game da batun, Heraldo Laura Gonzalez, shugaban Jaridar Reforma ta kasar Mexico ya jaddada muhimmancin cudanyar kafofin watsa labarai a yayin taron. Ya ce,

"tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Mexico da Sin a shekarar 1972, bangarorin biyu suna cude-ni-in-cude-ka a fannin tattalin arziki da cinikayya. Amma bisa girman kasuwannin kasashen biyu, akwai fannoni da dama da za su iya hadin kai, lallai wannan wata kyakkyawar dama ce gare mu. A madadin Jaridar Reforma ta kasar Mexico, ina so in bayyana a nan cewa, a matsayinmu na kafar watsa labarai, jaridarmu za ta yi kokarin da ba da gudummawa domin a san ainihin kasar Sin da ma kamfanonin kasar."

Idan muka waiwayi tarihi, muna iya gano cewa, tsohuwar hanyar siliki wata hanya ce ta cinikayya, baya ga yadda ta karfafa cudanyar al'adu. Tun da haka kakanin-kakaninmu suka yi, me ya sa muka kasa yi a yanzu? A halin yanzu da muke cikin saurin bunkasuwar tattalin arziki da dada ci gaban zaman al'umma, ya kamata mu ci gaba da bin hanyar siliki domin kasashen waje su kara fahimtar kasar Sin, da ma kara koyi da juna, ta yadda za mu samu makoma mai haske gaba daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China