in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta dauki sabbin matakan bude kofa in ji firaministan kasar
2018-09-19 19:18:03 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar sa za ta ci gaba da rage harajin fiton wasu hajoji da ake shigowa da su kasar, ta yadda hakan zai kara rage yawan harajin da kasar ke caza, kana ya kara yin kasa da wasu harajin da ake karba maras cikakkiyar fa'ida.

Firaministan na Sin, wanda ke tsokaci yayin bikin bude taron shekara shekara na masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki da ake wa lakabi da "Summer Davos", ya kara da cewa, shawara ce da Sin ta yanke, cewa za ta kara bude harkokin tattalin arzikin ta, domin bunkasa sauye sauye a fannin masana'antu, da kara ingantuwar ayyukan su, baya ga karin damammaki da hakan zai haifar ga masu sayayya na cikin gida. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China