in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoman jihar Pennsylvania ta Amurka sun ce takaddamar cinikayya ta jefa su cikin mawuyacin hali
2018-09-19 15:37:13 cri
Tankiyar cinikayyar dake tsakanin Amurka da Sin, wadda Amurka ta fara kaddamar wa, tana ta ci gaba har na tsawon watanni biyu. Amma har yanzu gwamnatin kasar Amurka na ci gaba da sanya sabon haraji kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Sakamakon takaddamar cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu, akwai manoman Amurka masu tarin yawa wadanda ke jin radadi a jikinsu, har wasunsu sun bayyana cewa, suna cikin mummunan hali sakamakon manufofin gwamnatin kasar kan harkokin cinikayya.

"Farashin amfanin gonanmu ya ragu da kashi 25 bisa dari, al'amarin da ya kara rage ribar da za mu samu".

William Boyd wani manomi ne dake jihar Pennsylvania ta kasar Amurka, yana da gonakin wake da masara a yankin Lehigh Valley dake jihar. Boyd ya ce, shi da sauran manoman wurin na jin radadi a jikinsu duba da irin manufofin cinikayya da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa. Saboda ba a sayar da wake da sauran amfanin gona zuwa kasar Sin da ma wasu sassan kasashen waje, tun daga watan Afrilun bana, farashin waken da ake sayarwa a kasuwannin cikin gidan Amurka ya ragu sosai. Duk da cewa an samu girbin wake mai yawa a yanayin kaka na bana, amma manoman Amurka ba yadda za su yi sai dai kawai su sayar da waken a farashi mai rahusa, hakan ya sa ba za su samu riba mai tsoka ba.

"Yanzu lokacin girbi ne, kuma amfani ya yi kyau. Amma ba yadda za mu yi, dole mu rage farashin wake da sauran amfanin gona, wato mu sayar da su a farashi mai sauki. Wata hanya kuma ita ce, mu ajiye amfanin gonanmu, har zuwa lokacin da farashinsu ya karu, sai mu sayar da su. Idan mun gudanar da cinikayya cikin 'yanci, bukatun da ake da su a cikin gida da waje za su taimaka wajen kara farashin amfanin gona."

Tun bayan da Amurka ta kaddamar da yakin cinikayya kan wasu kasashe, ciki har da Sin da Mexico da Canada, kasashe daban-daban sun dauki matakai don mayar da martani, ciki har da kara sanya kudin haraji kan amfanin gonan Amurka, ciki har da wake da naman alade da sauransu. Alkaluman kungiya kan waken da Amurka ke nomawa na nuna cewa, a baya, an fitar da kusan sulusin jimillar yawan waken Amurka zuwa kasar Sin a kowace shekara, amma yakin cinikayyar da sassan biyu ke yi a halin yanzu ya sa yawan waken da ake sayarwa zuwa kasar ya dada raguwa ainun.

Yayin da yake tsokaci kan kudin rangwamen da yawansa ya kai dala biliyan 12 da gwamnatin kasar Amurka ke shirin baiwa manoma, Boyd ya ce, shirin ya shafi wasu nau'o'in amfanin gona kadan ne, kana, yawan kudin rangwamen ba zai fitar da manoman daga cikin mawuyacin hali mai tsanani da suke ciki ba, kuma, ba zai sassauta babban matsin lambar tattalin arziki da manoman suke fuskanta ba sakamakon raguwar farashin amfanin gona. Boyd ya ce, shi da sauran manoman kasar Amurka, ba su bukatar kudin tallafi, kasuwanni kawai suke bukata, inda ya ce:

"Tun farko bana goyon bayan kaddamar da yakin cinikayya da Amurka ta yi kan kasar Sin. A baya, mun sayar da wake da masara masu tarin yawa zuwa kasar ta Sin, kuma mun samu riba mai tsoka. Amma tun lokacin da gwamnatin Trump ta kaddamar da yakin cinikayya, kome ya canja. Duk da cewa gwamnatinmu ta san matakin da ta dauka zai yi illa ga farashin amfanin gona, amma ta yi kunnen uwar shegu ta kaddamar da yakin cinikayya, kana ta yi watsi da muradun manoma."

Boyd ya kara da cewa, duba da taurin kai da gwamnatin Trump ta nuna gami da gazawar gwamnatin jihar Pennsylvania, manoman wake da masara da dama a wurin suna kokarin daukar matakai don daidaita matsalar da suke fuskanta. Alal misali, suna kokarin sayar da wasu amfanin gona zuwa wuraren kiwon alade da dabbobin daji, don sayar da su cikin farashin da ya dace. Amma, alade shi ma yana cikin amfanin gonan da aka kara sanyawa kudin haraji, don haka wannan mataki ba shi da amfani sosai.

Boyd ya ce, manoman kasar suna fatan gwamnatin Amurka za ta kawo karshen yakin cinikayyar da take yi da kasar Sin, don taimakawa ga bunkasuwar ayyukan gona na Amurka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China