in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kaddamar da rokar Long March-9 a shekarar 2028
2018-09-19 13:11:51 cri

Darektan sashen kula da harkokin injiniya na hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin Li Guoping ya bayyana cewa, kasarsa na shirin kaddamar da babbar rokar dakon kaya ta Long March mai lamba 9 a shekarar 2028.

Da yake karin haske, darekta Li ya ce, tsawon rokar ya wuce mita 90, sannan rokar na da kaurin mita 10, za kuma ta iya daukar kayan da ya kai nauyin tan 50 daga doron kasa zuwa duniyar wata.

Bugu da kari kasar Sin tana kera wani matsakaicin roka na Long March mai lamba 8, wanda ake saran harba shi sararin samaniya a karon farko a shekarar 2020.

Bayanai na nuna cewa, an harba rukunin rokar Long march zuwa sararin samaniya sau 284, inda suka yi jigilar sama da kumbuna 400 zuwa sararin samaniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China