Huang Kunming ya bayyana hakan ne jiya Talata yayin da yake jawabi a taron dandalin kare hakkin dan-Adam na wannan shekara da aka bude a birnin Beijing na kasar Sin.
Ya ce, har kullum JKS da ma gwamnatin kasar na mutunta da kuma kare hakkin dan-Adam. Yana mai cewa a cikin sama da shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta hade manufofi da suka shafi batun kare hakkin bil-Adam da yanayin da kasar ke ciki a zahiri
Dandalin da aka fara shiryawa a shekarar 2008, a bana ya samu halartar jami'ai da masana da muhimman mutane sama da 200 daga kimanin kasashe da yankuna 50 da ma kungiyoyin kasa da kasa.(Ibrahim)