in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC ta haramta amfani da wayar salula a rumfunan zabe
2018-09-18 15:15:21 cri
Labarin da jaridar Leadership a yau ta bayar ya nuna cewa, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce ba za a bari masu jefa kuri'a su shiga rumfunan zabe da wayar hannu ko duk wata na'urar da za ta iya daukar hoto ko bidiyo da ita ba.

Shugaban Hukumar ya bayyana haka ne a jiya yayin da yake jawabi a garin Osogbo a wurin wani taron da masu ruwa da tsaki suka shirya kan zaben gwamnan Jihar Osun. An shirya zuwa ranar Asabar din nan mai zuwa ne za a gudanar da zaben gwamna a Jihar ta Osun. Shugaban hukumar zaben ya ce, wannan matakin da hukumar INEC ta dauka zai taimaka wajen magance matsalar sayan kuri'u da sayar da kuri'un da ake fama da shi a fadin Nijeriya.

Shugaban ya kara da cewa, ba za a hana masu jefa kuri'a yin amfani da na'urorin nasu ba a wuraren jefa kuri'ar, amma ba za a bari su rike ababen daukan hoto da wayoyin hannu ba da zaran an tantance su an ba su takardun dangwala zaben har sai sun jefa kuri'arsu a cikin akwati sannan za su samu damar yin duk abin da suka ga dama da wayar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China