in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harbe Sinawa biyu har lahira a jamhuriyar Congo
2018-09-17 11:04:01 cri
Ofishin jakadancin Sin dake kasar jamhuriyar Congo ya tabbatar a jiya Lahadi cewa, an harbe wasu Sinawa biyu har lahira a daren ranar 14 ga wannan wata a kusa da birnin Brazzaville.

Bayan da aka gudanar da bincike a wurin, rundunar 'yan sandan kasar ta tabbatar da cewa, an harbi wata mota dake kan hanyar zuwa birnin Brazzaville a wurin dake da nisan kilomita 70 a arewa da birnin, abin da ya haddasa mutuwar mutane 3 tare da raunata mutum daya, mutane biyu daga cikin mutanen uku da suka mutu ma'aikata ne daga kasar Sin.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa, ba a kai ga gano maharin da ma dalilin da ya sa aka kai harin ba, amma an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Bayan faruwar lamarin, jakadan Sin dake jamhuriyar Congo Ma Fulin ya tuntubi hukumomin jamhuriyar Congo da abin ya shafa, tare da yin kashedin tabbatar da tsaro ga kamfanonin Sin da Sinawan dake kasar. Ban da wannan kuma, ofishin jakadancin Sin dake kasar ya tattauna da ma'aikatar harkokin cikin gida ta jamhuriyar Congo da jami'an hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa, inda ya kalubalance su da su hanzarta kama maharin, tare da daukar matakan tabbatar da tsaron kamfanonin Sin da ma Sinawa dake kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China