Mohamed Hussein Abdille wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan, ya ce, sakamakon goyon bayan da kasashen nahiyar suka samu daga kasar Sin, yanzu haka shugabanin kasashen nahiyar suna iya tafiyar da harkokin kasashensu ba tare da tuntubar tsoffin kasashen da suka yi musu mulkin mallaka ba.
Yayin da alakar sassan biyu ke ci gaba da bunkasa a 'yan shekarun nan, wasu kasashen yammacin duniya na cewa, kasar Sin na jibgawa kasashen Afirka bashi ne, domin ta samu tasiri na siyasa da ma kwashe albarkatun da Allah ya horewa nahiyar
Jamai'in ya ce gwamnatin kasar Sin ba ta taba tilastawa kowa ce kasa karba rance ba. Gwamnatocin kasashen Afirka ne suka sanya hannu kan yarjeniyoyin rance bisa radin kansu domin gudanar da ayyukan raya kasashen su.
Ya ce, kasashen nahiyar sun dade suna karbar tallafi da rance daga kasashen yamma, amma nahiyar ba ta samu ci gaba kamar yadda take a halin yanzu ba. Bugu da kari, kasashen yamma sun sha gallazawa kasashen na Afirka a lokacin da suke yi musu mulkin mallaka. (Ibrahim)