in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakada: Taron FOCAC ya taimakawa kyautata yanayin da ake ciki a duniya
2018-09-14 13:24:24 cri


Jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo, ya kira wani taron manema labaru a birnin Alkahira a ranar Laraba da ta gabata, inda ya yi bayani kan sakamakon da aka samu, a wajen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a farkon watan Satumban da muke ciki.

Jakada Song Aiguo ya raka shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi kasar Sin, yayin ziyarar da ya kai kasar ta baya bayan nan, domin halartar taron koli na FOCAC. Kan taron da ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, jakada Song ya bayyana cewa, akwai shugabannin kasashe 10, da firaminista 40, duk daga nahiyar Afirka, da suka halarci wannan taro, inda suka shaida yadda aka kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa fiye da 150.

Daga bisani, jakada Song na kasar Sin, ya yi tsokaci kan manufar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wajen taron mai taken "manyan matakai guda 8", inda ya ce:

"Wannan manufa ta shafi wasu fannonin da kasar Sin da kasashen Afirka suka dade suna hadin kai da juna a kai, kana ta sanya an samu karin damammakin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, inda ta wannan manufa, aka kafa wani cikakken tsari domin nasarar matakan hadin kai na nan gaba."

Song ya kara da cewa, cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin Xi Jingping, ya ambaci wasu manufofi na tushe da kasar Sin take bi, a kokarin kyautata huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka. Haka zalika, ya jaddada burinsa na kulla wata al'umma mai makomar bai daya tsakanin bangarorin Sin da Afirka. Jawabin da shugaban ya yi a farkon taron ya tabbatar da wani yanayi mai armashi, abin da ya sa aka zartas da wasu takardu masu muhimmanci guda 2, wadanda suka zama muhimmin sakamako na taron. Cikin takardun 2, "Sanarwar Beijing" ta nuna ra'ayi daya da Sin da kasashen Afirka suka samu bisa wasu batutuwa masu muhimmanci dake haifar da tasiri ga duniya. Sa'an nan, wani "Shiri kan matakan da za a dauka" da aka gabatar wajen taron, ya bayyana wasu matakan hadin gwiwa da za a dauka cikin shekaru 3 masu zuwa. Bayan da ya yi bayani kan wadannan sakamakon da aka samu a wajen taron FOCAC na wannan karo. Jakada Song ya yi tsokaci kan ma'anar taron, ta la'akari da yanayin da ake ciki na samun sauye-sauyen fasalin siyasar duniya, inda ya ce:

"Kasar Sin da kasashen Afirka a hade suke, sun bayyana ra'ayinsu na kin amincewa da ra'ayin yin gaban kai, da na kariyar ciniki, da jaddada bukatar kare tsarin lura da ra'ayoyin bangarori daban daban, da na ciniki cikin 'yanci. Ta haka, an nuna wani ra'ayi mai yakini ga kokarin tinkarar yanayin rashin tabbas da ake fama da shi a duniya."

A cewar Song, wannan kyakkyawan sakamakon da aka samu wajen taron kolin FOCAC na Beijing ya sa shugabannin kasashen Afirka mahalartar taron suka gamsu sosai. Song ya ce,

"Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron, sun nuna yabo game da huldar dake tsakanin Sin da Afirka mai tarihi, wadda ke ta samun ci gaba, duk da sauyawar yanayin siyasa da ake samu a duniya. Sun kuma gode wa kasar Sin, game da yadda take kokarin rufa wa kasashen Afirka baya, don neman ganin sun kau da talauci, da samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa."

Ban da haka, jakada Song ya yi tsokaci kan ziyarar da shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi ya kai kasar Sin a wannan karo. A cewarsa, wannan ziyara na tare da dimbin sakamako, musamman ma a fannin karfafa huldar abota dake tsakanin kasashen Sin da Masar. A yayin da shugabannin bangarorin 2 ke ganawa da juna, sun dora muhimmanci ga batun gudanar da ayyuka na hadin kai. Sa'an nan sun cimma matsaya a fannonin daukar matakai karkashin shawarar "Ziri daya da Hanya daya", da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 a fannin raya masana'antu. Haka zalika, shugabannin kasashen 2 sun gane wa idanunsu yadda aka daddale jerin yarjeniyoyi, don habaka hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen 2 a nan gaba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China