in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin duniya sun yi ban kwana da marigayi Kofi Annan
2018-09-14 10:36:16 cri
Shugabannin kasashen Afrika da ma na duniya da dama suka bi sahon shugaban kasar Ghana Nana Aakufo-Addo a jiya Alhamis domin yin ban kwana da tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan, wanda ya rasu a kasar Switzerland a ranar 18 ga watan Augasta.

Daga cikin shugabannin da suka halarci bikin binne marigayin wanda gwamnatin kasar Ghana ta shirya, sun hada da babban sakataren MDD mai ci Antonio Guterres, da Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d'Ivoire, da Julius Maada Bio na kasar Saliyo.

A bayanansa na nuna yabo, shugaban kasar Ghana Akufo-Addo ya bayyana Annan a matsayin mutum mai mutunci, mai kishin al'ummar duniya, mai basira, kuma mutum ne mai kima a idanun duniya.

"Mutum ne mai taka-tsan-tsan, mai alfahari da Afrika, mai son zaman lafiya, kuma cikakken masanin al'amurran diplomasiyya. Kalmomi ba za su iya bayyana kimar Kofi Annan ba, wani babban gwarzo ne da tarihi ba zai manta da shi ba," in ji Akufo-Addo.

Sama da mutane 1,600 ne suka cika babban dakin taron jama'a wanda ke iya daukar mutane 500 domin nuna alhininsu, yayin da daruruwan kafafen yada labaru daga sassan duniya suka watsa bikin binne marigayin.

A kalamansa na nuna yabo, sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce kamar wanda ya gabace shi Dag Hammarskjold, mista Annan ya taka muhimmiyar rawa wajen sauke nauyin dake wuyansa na kyautata shugabancin MDD don cigaban duniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China