in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki na gabashin duniya karo na hudu
2018-09-12 21:07:03 cri

Yau Laraba aka bude cikakken taro karo na hudu na dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki na gabashin duniya a garin Vladivostok na kasar Rasha, wanda ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Mongolia Khaltmaa Battulga da firaministan kasar Japan Shinzo Abe da kuma firaministan kasar Koriya ta Kudu Lee Nak-yon.

A jawabinsa yayin taron, shugaba Xi Jinping jaddada cewa, kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasashen da ke yankin wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da cimma moriyar juna da samun nasara tare, da kyautata dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen, da ma samun bunkasuwa cikin daidaito, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a yankin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, ko da yaushe kasar Sin na mara wa Rasha baya wajen gudanar da aikin raya yankin gabas mai nisa na Rasha. A 'yan shekarun da suka gabata, an samu sakamako mai kyau a hadin gwiwar Sin da Rasha a yankin gabas mai nisa .Xi ya kara da cewa, bana da kuma badi su ne shekarun cudanyar wuraren kasashen biyu wanda shi da Shugaba Putin suka tabbatar, lamarin da zai kyautata hadin gwiwar bangarorin biyu a yankin gabas mai nisa. Ya ce,

"kasar Sin na son hada kai tare da Rasha wajen inganta hadin kansu a fannonin raya muhimman ababen more rayuwa, makamashi, ayyukan gona, da ma yawon shakatawa, musamman yadda za su karawa kamfanoni matsakaita da kanana kwarin gwiwar inganta harkokin fasaha da karin ingancin kayayyaki, a kokarin taimakawa juna wajen samun moriya tare da ma kyawawan sakamakon a hadin kansu."

Ban da wannan, Shugaba Xi ya jaddada cewa, yankin arewa maso gabashin Asiya mai jituwa, inda ake samun amincewar juna da hadin kai sosai da ma kwanciyar hankali ya dace da muradun kasa da kasa da ma fatan duniya, wanda kuma zai ba da muhimmiyar ma'ana wajen kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da ma raya dokokin kasa da kasa yadda ya kamata. A matsayinta na kasa da ke yankin, Sin na son ci gaba da kokari a wannan fannin. Xi yana mai cewa,

"ko da yaushe Sin na da ra'ayin samun bunkasuwa cikin lumana. Tana kokarin sada zumunta da kasashen da ke makwabtaka da ita, da shiga a dama da ita cikin aikin hadin kai na yankin bisa zummar ba da gudummawa, gami da himmatu wajen yin tattaunawa tsakanin kasashen dake yankin. Kasar Sin za ta kara hada kai tare da sauran kasashen duniya wajen neman hanyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a arewa maso gabashin Asiya, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba a yankin."

Game da batun kyautata hadin kai, Shugaba Xi ya furta cewa, ya kamata bangarori daban daban su hada shirye-shiryensu na raya kasa tare, da kara yin mu'amala kan manufofi domin tabbatar da fannonin hadin kansu. Ya ce,

"ya kamata mu ba da muhimmanci kan raya muhimman ababen more rayuwa da ke shafar kasashen biyu, da samar da 'yanci da saukaka harkokin cinikayya da zuba jari, domin raya tattalin arziki na yankin mai salon bude kofa. Ban da wannan ya kamata mu yi kokarin hada kai da wasu kasashe wajen aiwatar da shirye-shirye da suka dace, domin amfana wa jama'a."

Haka zakila Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata a tattauna domin bullo da wani sabon salon raya yankin arewa maso gabashin Asiya, da mai da hankali kan kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da ma kiyaye muhalli, a kokarin samun tsarin masana'antu mai tsimin makamashi da kare muhalli.

A nasa bangare, Shugaba Putin ya nuna godiya ga Shugaba Xi da sauran shugabanni da suka halarci taron, inda ya nuna yabo kan cewa, hadin kan Rasha da Sin a yankin gabas mai nisa na Rasha na da kyakkyawar makoma. Ya kuma kara da cewa, Yankin gabas mai nisa na bude kofa ga waje, Rasha na maraba da kamfanonin kasa da kasa wajen zuba jari da raya ayyuka a yankin. Ita ma Rasha na son kyautata hadin kai tare da bangarori daban daban na yankin arewa maso gabashin Asiya don samun moriyar juna da ma sakamako mai kyau.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China