A jawabin da ya gabatar, jakada Ma ya ce, cin hanci da rashawa tamkar makiyi ne ga jama'ar fadin duniya. Haka kuma rage duk wani yunkuri na bayar da cin hanci da karbar toshiya gami da kara karfin maido da dukiyoyin da aka sata, na daga cikin muradun neman ci gaba da MDD ke son cimmawa nan da shekara ta 2030. Ma ya ce, ya zama dole kasashen duniya su rubanya kokarin karfafa hadin-gwiwa don yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda ba za'a iya baiwa mutane damar bayar da cin hanci da karbar toshiya ba.(Murtala Zhang)