in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Manufar da kasar Rasha ta dauka ta mai da hankali kan gabashin duniya
2018-09-11 19:14:23 cri

Daga ranar 11 zuwa ta 13 ga watan Satumban da muke ciki, za a gudanar da dandalin tattaunawar batun tattalin arziki na yankin gabashin duniya karo na 4 a birnin Vladivostok dake gabashin kasar Rasha. Mahalarta taron za su hada da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwarorinsa na wasu kasashen dake arewa maso gabashin Asiya. Ban da haka, tawagogi daga kasashe fiye da 60 su ma za su halarci taron. Wannan yanayi na samun halartar shugabanni da manyan jami'ai, da kuma tawagogi na kasashe da yawa, ba a taba ganin irinsa ba bisa tarihin taron.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin shi ne ya ba da shawarar kafa dandalin tattaunawar a shekarar 2015. Wannan shawara ita ce daya daga cikin manufofin kasar Rasha na "karkata ga gabashin duniya", wadanda kasar ta dauka don tinkarar yanayin da ake ciki na samun lalacewar huldar dake tsakaninta da kasashen Turai gami da kasar Amurka. A idanun kasashen dake yammacin duniya, manufar da kasar Rasha ta dauka, tana tare da burin "daidaita manufa cikin wani dan gajeren lokaci" don saukaka matsin lamba da take samu sakamakon takunkumin da aka sanya mata. Har ma wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun nuna shakku cewa, "ta hanyar karkata ga gabashin duniya kawai, kasar Rasha za ta samu damar kyautata makomarta? " Sai dai yadda kasar Rasha ta gaggauta aikin hadin gwiwa da kasashen dake gabashin duniya cikin shekarun baya, ya shaida cewa, matakin "karkata ga gabashin duniya" ya riga ya zama daya daga cikin manyan manufofin kasar na dogon lokaci.

Kasar Rasha na fahimtar babbar moriyar da ta samu wajen karfafa hadin-gwiwa da kasar Sin. A matsayinta na babbar kasa ta farko da ta yi harkokin kasuwanci da Rasha, kasar Sin ta kan tura wata babbar tawagar dake kunshe da manyan jami'an gwamnati, don halartar taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasashen gabashin duniya a kowace shekara tun irin wannan taro karo na farko wanda aka yi a shekara ta 2015. Bana ta kasance shekara ta farko da shugaban kasar Sin ya halarci wannan taron dandalin tattaunawar, al'amarin da ya nuna cewa, kasar Sin na da babbar niyya wajen inganta hadin-gwiwa da Rasha don raya yankin gabas mai nisa na Rasha.

Hadin-gwiwar kasashen Sin da Rasha ta fuskar raya yankin gabas mai nisa na Rasha, na kara taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu. A halin yanzu a yankin gabas mai nisa na kasar Rasha, Sin ta kasance babbar kasa ta farko wajen yin kasuwanci da wurin, kana babbar kasa ta farko da ta zuba jari a yankin, jarin da ya kai kimanin dala biliyan hudu. Haka kuma akwai kamfanonin kasar Sin guda 26, wadanda suka shiga cikin yankin TOP da Rasha ta kafa musamman don raya yankin gabas mai nisa, gami da tashar jiragen ruwa dake Vladivostok. Har wa yau, Sin da Rasha suna nan suna kokarin gina wasu muhimman ayyukan da suke kan kogin Heilongjiang, wanda ya ratsa ta bakin iyakokin kasashen biyu, ciki har da layukan dogo da hanyoyin mota, tare da zummar inganta mu'amala da cudanya tsakanin muhimman ababen more rayuwar jama'a na kasashen biyu. Babu tantama, zurfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Rasha, wani muhimmin fanni ne na manufar Rasha ta mai da hankali kan gabashin duniya.

Ban da wannan, kasar Rasha ta gano kyakkyawar makoma ta habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen dake arewa maso gabashin Asiya. Ya zuwa yanzu, an riga an cimma nasarar gudanarwar taron dandalin tattaunawar batun tattalin arziki na yankin gabashin duniya karo guda uku, wadanda suka haifar da kyakkyawan tasiri a yankin arewa maso gabashin Asiya, har an kai ga kulla yarjejeniyoyi masu darajar kudin Rasha RUB biliyan 2500, kana ana sa ran adadin zai wuce RUB biliyan 3500 a shekarar bana.

Yankin arewa maso gabashin Asiya na da albarkatu da dama, kuma yana da kasuwanni masu kyau. Ban da shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugabannin kasashen Mongoliya, Japan da Koriya ta Kudu da dai sauransu za kuma su halarci taro na wannan karo, lamarin da ya nuna aniyar kasashen wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A halin yanzu, ana dukufa wajen tsara shirye-shiryen ciniki dake tsakanin kasashen biyu, ko kuma kasashe da dama a yankin arewa maso gabashin Asiya, kamar hanyar tattalin arziki ta Sin, Rasha da Mogoliya da ake dukufa wajen ginawa, da yarjejeniyar 'yancin ciniki da ake sa ran kullawa a tsakanin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki da ake fatan kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu za su yi a hukumance da dai sauransu.

A sa'i daya kuma, kasashen arewa maso gabashin Asiya sun nuna amincewa kan shirin "Ziri daya da hanya daya", sabo da haka, halartar shugaba Xi Jinping cikin taron za ta ba da gudummawa wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen da abun ya shafa, da kuma inganta shirin "Ziri daya da hanya daya" a yankin arewa maso gabashin Asiya. Haka kuma, lamarin zai ba da taimako ga kasar Rasha wajen cimma burinta na raya yankin gabas mai nisa nata.

Bugu da kari, kasar Rasha ta gano damar samun ci gaba sakamakon saurin bunkasuwar tattalin arzikin yankin Asiya da Pasific. Yankin gabas mai nisa na Rasha na da yawan albarkatun halittu, wanda ake kiransa "wuri guda kacal a duniya mai dauke da albarkatun da ba a binciko ba". Amma har zuwa yanzu yankin nan bai nuna ma'anarsa a fannin manyan tsare-tsare da darajarsa a fannin tattalin arziki ba, sakamakon rashin ci gaban tattalin arziki da karancin manyan kayayyakin morewa rayuwa, da kaura da mazauna yankin ke yi da dai sauransu. Bisa la'akarin da aka yi kan neman daidaito a tsakanin gabas da yamma, a shekarun nan kasar Rasha ta kai ayyukan raya yankin gabas mai nisa, zuwa matsayin na manyan tsare-tsaren kasar.

Dalilin da ya sa Rasha ta tsara wannan shiri, shi ne domin saurin ci gaban tattalin arzikin yankin Asiya da Pasific. A matsayinsa na daya daga cikin yankunan da suka fi samun saurin ci gaban tattalin arziki a duniya, yankin Asiya da Pasific yana kasancewa babbar kasuwa ga kasar Rasha, kuma wurin da kasar za ta yi kokarin samun jari. Ana raya yankin gabas mai nisa ba domin biyan bukatun kasar ta Rasha, na neman ci gaban tattalin arziki da al'umma kawai ba, har ma za a sanya kasar ta samu bunkasuwa sakamakon saurin ci gaban tattalin arziki na yankin Asiya da Pasific. Bisa kididdigar da hukumar kwastan kasar ta yi, an ce, kason jimilar cinikayya a tsakanin Rasha da kasashe mambobin kungiyar APEC bisa na jimilar cinikayyar wajen kasar ya karu daga kashi 20% a shekaru 10 da suka gabata, zuwa kashi 31% na shekarar 2017. Bisa wani binciken ra'ayin jama'a da aka yi a shekarar 2016, kashi 70% na jama'ar kasar ta Rasha na ganin cewa, kasar na aiki mai kyau da yawa, fiye da maras kyau wajen hada kai tsakanin kasarsu da kasashen yankin Asiya da Pasific.

Abin da ya kamata mu lura shi ne, manufar maida hankali kan kasashen gabashin duniya da kasar Rasha ta dauka, ba manufa ba ce da aka fitar domin tinkarar takunkumin da kasashen yammacin duniya ke sanyawa kasar Rasha, amma tsanantar dangantakar dake tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya ya sa kaimi ga kasar Rasha wajen kara maida hankali kan gabashin duniya. Ko da haka, nahiyar Turai muhimmiyar abokiyar cinikayya ce ta kasar Rasha, yawan cinikin da aka yi a tsakanin Rasha da kasashen kungiyar EU ya kai fiye da kashi 40 cikin dari, bisa na adadin yawan cinikayya a tsakanin Rasha da kasashen waje. Sabo da hakan, kasar Rasha ba za ta yi watsi da kasashen yammacin duniya ba, musamman cewa ba za a gaza yin hadin gwiwa tare da kasashen Turai ba. Kasar Rasha za ta maida hankali ga gabashi da yammacin duniya gaba daya, kamar yadda ungulu mai kai biyu kan alamar dake shaida kasar Rasha ya kalli bangarori biyu. Amma bisa yanayin da ake ciki, Rasha za ta fi samun kyakkyawar makoma idan ta kara maida hankali kan gabashin duniya. (Bello, Murtala, Maryam, Bilkisu, Zainab, ma'aikatan Sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China