in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin ya samu nasarori ta hanyar yin kirkire-kirkire
2018-09-11 14:05:28 cri

A watan Maris na bana, bisa shirin yin kwaskwarima kan hukumomin kwamitin jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar, an kafa babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, inda aka fara yin amfani da wannan suna tun daga ranar 19 ga watan Afrilu a hukunce. Kamfanin watsa labarai na CMG ya hada da gidan telebijin na CCTV da CGTN da gidan rediyon jama'ar kasar Sin wato CNR, da kuma gidan rediyon kasar Sin na CRI.

Bayan gudanar da kirkire-kirkire na kokarin samun bunkasuwa tare a wasu watannin da suka gabata, an inganta karfin watsa labaru da jawo hankali da fada gaskiya ga jama'a, kana kuma an samu babban ci gaba kan sabbin hanyoyin watsa labaru da telebijin, da kuma watsa labaru ta yanar gizo.

Bayan da aka kafa babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, an yi kokari wajen hada gidajen watsa labaru yadda ya kamata. Masu jagorancin shiri na gidajen watsa labaru na CCTV da CNR da CRI sun yi hadin gwiwa a karo na farko, wajen jagorancin shiri tare a karo na farko ne game da dandalin tattaunawa na Boao na Asiya.

A gun taron koli na birnin Qingdao na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da aka gudanar a watan Yuni na bana, sashen watsa labaru na CCTV ya gabatar da shirin musamman mai suna "birnin Qingdao na maraba da zuwan abokai", wanda aka gabatar da shi kai tsaye a gidan CNR da CRI a sa'i daya tare a karo na farko.

Kana kamfanin CMG ya gaggauta watsa labaru ta sabbin hanyoyi. A ranar 22 ga watan Afrilu, kamfanin CMG ya halarci taron koli na fasahohin sadarwa na zamani na kasar Sin karo na farko, inda aka shaida nasarorin da gidan CMG ya samu wajen raya sabbin hanyoyin watsa labaru ta fasahohin sadarwa na zamani da na yanar gizo.

A watan Afrilu, kamfanin telebijin na kasa da kasa na Sin dake karkashin jagorancin gidan CMG, ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwar fasahohin zamani tare da kamfanin Alibaba, ta haka bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa a fannonin dandalin sadarwa, da tattara sako, da manhaja ta wayar salula da sauransu.

A ranar 31 ga watan Yuli, kamfanin telebijin na kasa da kasa na Sin, ya kaddamar da hadin gwiwa tare da kamfanin China Mobile Communications Corporation a fannonin nazarin fasahohin zamani na 5G, da kafar telebijin mai inganci ta 4K, da watsa labaru ta bangarori daban daban, da tattara sako da kuma jari da sauransu, ta haka za a more albarkatu da yin amfani da fifikonsu, da kuma samun moriyar juna. A ranar 1 ga watan Agusta, kamfanin CMG ya yi mu'amala sosai tare da kamfanin Sina, wadanda suka cimma daidaito kan fadada aikin watsa labaru ta yanar gizo.

Ban da watsa labaru da raya sha'anin watsa labaru, kamfanin CMG ya hada kan manyan kafofin watsa labaru uku, wajen gudanar da aikin amfanin jama'a tare, inda aka samu nasarori masu yawa. Tun daga watan Yuli na shekarar 2018 zuwa watan Yuni na shekarar 2019, kamfanin CMG zai kara zuba jari da kudin Sin RMB Yuan biliyan daya, bayan da ya riga ya zuba jari Yuan biliyan 1 da miliyan 40 wajen gabatar da shirye-shiryen taimakawa yaki da talauci, don sa kaimi ga yankunan Sin da dama su cimma burin kawar da talauci.

Bayan da aka kafa kamfanin CMG, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen CCTV ya karu cikin sauri, kana yawan mutane da suka kalli shirye-shirye ta yanar gizo ya karu sosai. A yayin gasar cin kofin duniya ta FIFA ta bana, yawan mutanen da suka kalli gasar ta yanar gizo ta CMG ya kai fiye da miliyan 9, tun daga rana ta farko da aka fara gasar. Kuma a ranar 18 ga watan Yuni, yawan mutanen da suka kalli gasar ta yanar gizo ta CMG ya kai fiye da miliyan 50.

A matsayin dandalin watsa labaru na kasar Sin, gidan CMG yana kokarin raya sha'anin watsa labaru ta hanyoyi daban daban bayan da aka kafa shi, kana yana kokarin neman kyautata tsarin raya sha'anin watsa labaru, don cimma burin kafa dandalin watsa labaru na zamani mafi kyau a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China