in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun yi maraba da matakan daidaita rikicin yankin arewa maso gabashin Afrika
2018-09-09 16:00:03 cri

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi marhabun da ziyarar da ministocin wajen Eritrea, Habasha da Somaliya suka kai zuwa Djibouti, inda ya bayyana ziyarar da cewa, tamkar wani muhimmin mataki ne a kokarin warware sabanin dake tsakanin kasashen shiyyar arewa maso gabashin Afrika.

Cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, Guterres ya ce, matsayar da ministocin harkokin wajen kasashen 4 suka dauka na yunkurin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, wani babban misali ne na ci gaban da aka samu a yankin, har ma da wajen nahiyar Afirka baki daya.

Ya jaddada cewa, MDD a shirye take ta goyi bayan kasashen dake shiyyar domin tabbatar da cimma nasarar da aka sanya a gaba na yin hadin gwiwa don samun dawwamamman zaman lafiyar shiyyar.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AUC), Moussa Faki Mahamat, a jiya Asabar ya yi maraba da ci gaban da aka samu na baya bayan nan a shiyyar arewea maso gabashin Afrika wajen kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen shiyyar.

Cikin wata sanarwa, hukumar AUC ta ce, Faki ya yabawa shugabannin kasashen Djibouti, Eritrea, Habasha da Somalia bisa jajurcewar da suka nuna da kuma sadaukar da kai wajen sanya muradun al'umma da yankunansu sama da duk wata bukata.(Ahmad fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China