in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kaddamar da jerin matakan inganta hadin kan tattalin arziki da cinikayya da Afirka
2018-09-08 18:06:41 cri

An cimma jerin nasarori da dama wajen inganta hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai da aka kammala ba da dadewa ba a nan birnin Beijing.

Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin na cewa, nan gaba kasar Sin za ta kaddamar da matakai da dama, don tabbatar da hadin kai tsakaninta da kasashen Afirka ta fuskokin zuba jari da tattalin arziki da cinikayya.

A gun taron manema labarun da ma'akatar cinikayyar kasar Sin ta shirya a 'yan kwanakin baya, kakakin ma'aikatar Gao Feng ya bayyana cewa, kasar Sin ta za yi kirkire-kirkire kan tsarin hada kanta da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kuma za ta kafa tsarin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka, don bude sabuwar hanyar gudanar da hadin kai a fannonin da dama tsakanin kasar, musamman ma kananan hukumomin kasar da kasashen Afirka. Baya ga haka, za a kara raya yankin hadin kan tattalin arziki da cinikayya, inda za a nuna goyon baya ga kamfanoni daban daban da su kafa yankunan hadin kan tattalin arziki da cinikayya, wadanda ke iya samar da alfanu ta fuskokin tattalin arziki da rayuwar al'umma. Kana za a kara karfafa gwiwar kamfanoni don su habaka tare da zuba jari a kasashen Afirka.

A waje guda kuma, mista Gao Feng ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi amfani da wasu ayyuka, ciki har da bikin baje kolin shigo da kayayyaki na kasa da kasa na kasar Sin, da bikin baje kolin kamfanonin kasar Sin da dai sauransu, da kuma tsarin hadin kai a fannin cinikayyar yanar gizo, don ciyar da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba.

"Kasar Sin za ta yi amfani da dandalin bikin baje koli na shigar da kayayyaki na kasa da kasa na Sin, don inganta shigo da kayayyakin kasashen Afirka zuwa kasar Sin. Za kuma ta nuna goyon baya ga majalisun cinikayya da kamfanonin kasar, don su je kasashen Afirka su shirya bikin baje kolin tamburan kayayyaki kirar kasar Sin a ko wace shekara, ta hakan za a shigar da kayayyaki masu inganci kirar kasar Sin Afirka, a waje guda kuma za ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka don su gudanar da ayyuka daban daban na inganta cinikayya. Baya ga haka, Sin za ta tattauna tare da kasashen da abun ya shafa kan kafa tsarin hadin kai na cinikayyar yanar gizo tsakanin Sin da Afirka, da kara cimma matsaya kan manufofi, hada kan shirye-shirye, more fasahohin da aka samu, da yin nazari tare da kuma horar da kwararru."

An ce, a ranar 2 ga wata, kasashen Sin da Mauritius suka kawo karshen shawarwari kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci a tsakaninsu, wannan ita ce yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci ta farko da Sin ta sa hannu tare da wata kasar Afirka. Game da haka, mista Gao Feng ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta shafi fannoni da dama, ciki har da cinikayyar kayayyaki, cinikayyar ba da hidima, zuba jari da hadin kan tattalin arziki da dai sauransu. A cewarsa,

"A fannin cinikayyar kayayyaki, yawan kason kayayyakin bangarorin biyu da ake shige da fice su, wadanda ba za a karbi haraji ba, da yawan kason kudaden da suka samu wajen yin cinikayyar kayayyakin da ba za a karbi haraji ba dukkaninsu za su wuce kashi 90 cikin 100, a fannin ba da hidima kuma, bangarorin biyu sun yi alkawarin cewa, za su bude hukumomi sama da 100. A fannin zuba jari, za a kara daukaka matsayin yarjejeniyar ba da kariya ga zuba jari a tsakanin Sin da Mauritius da aka cimma a shekarar 1996, wannan ne karon farko da Sin ta kara matsayin yarjejeniya irin wannan tare da kasashen Afirka."

Mista Gao Feng ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tattaunawa da yin shawarwari kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tare da kasashen Afirka da kungiyoyin shiyyar dake da burin yin haka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China