in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce zai samu wasikar da shugaban Koriya ta Arewa ya rubuta masa
2018-09-08 16:50:42 cri
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya bayyana jiya Jumma'a cewa, zai samu wasikar da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un, ya rubuta masa, ya na mai cewa wasikar za ta kunshi abubuwa masu gamsarwa.

Trump ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, Koriya ta Arewa ta gabatar da wasikar ne a bakin iyakarta da Koriya ta Kudu, inda sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, zai tafi da ita kasarsa. Trump ya kara da cewa, ya gamsu sosai da ra'ayoyin da Koriya ta Arewa ta bayyana kwanakin baya dangane da Amurka, gami da batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriyar, kuma an cimma wasu nasarori da dama game da shawarwari tsakanin Amurkar da Koriya ta Arewa.

Tun a ranar 24 ga watan Augusta, Donald Trump ya sanar da soke ziyarar da Mike Pompeo zai kai Koriya ta Arewa. Daga baya a ranar 5 ga watan Satumba kuma, Kim Jung-un ya gana da tawagar shugaban kasar Koriya ta Kudu a birnin Pyongyang, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tsaya haikan kan kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da cimma maslaha da Koriya ta Kudu dangane da ajandar shawarwarin da kasashen 2 za su yi a watan da muke ciki a Pyongyang. Tuni a ranar 6 ga wata, Trump ya yabawa kalaman Kim Jung-un ta shafinsa na sada zumunta, inda ya ce, Amurka na son yin kokari tare da Koriya ta Arewa, don cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China