in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sa hannu kan takardun fahimtar juna game da "Ziri daya da hanya daya" tare da kasashen Afirka 37 da AU
2018-09-07 19:34:13 cri
Mataimakin shugaban sashen hadin kai da kasa da kasa, na kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Xia Qing, ya bayyana a yau Juma'a cewa, ya zuwa ranar 6 ga wata, kasar Sin ta riga ta sa hannu kan takardun fahimtar juna game da shawarar "Ziri daya da hanya daya"tare da kasashen Afirka 37, baya ga kungiyar tarrayar kasashen Afrika wato AU. Kaza lika yawan kasashen sun kai kashi 70 cikin dari bisa jimillar kasashen nahiyar 53 da suka halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka shirya a nan birnin Beijing.

An ce, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta sa hannu kan takardun hadin kai game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" har guda 123, tare da kasashe 105 dake Asiya, da Afirka, da Turai, Latin Amurka, da kudancin Pacific. A waje guda kuma, ta sa hannu kan takardun hadin kai guda 26 tare da kungiyoyin kasa da kasa 29.

Mista Xia ya bayyana cewa, a nan gaba za a yi kokarin aiwatar da takardun da aka cimma, da nufin samun hakikanin sakamako cikin sauri. Hakan zai kuma sanya kasashen Afirka, da jama'arsu, su ci gajiya sakamakon nasarorin da aka cimma wajen aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China