in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Sin da Afirka kawance na gaskiya da babu iyaka
2018-09-07 10:46:31 cri

Nahiyar Afirka wadda ke kunshe da galibin kasashe marasa ci gaba, tana kokarin samun gurbin da ya dace da ita a duniya, kuma matakan da kasar Sin ke dauka ya nuna irin gagarumar gudummawar da take bayarwa ga ci gaban kasashen na Afirka.

Yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana daga ranakun 3 da 4 ga watan Satumban da muke ciki a birnin Beijing na kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zayyana wani sabon tsari game da alakar Sin da kasashen na Afirka, ciki har da wasu sabbin matakai guda 8, matakan da mahalarta taron suka yi maraba da su.

Bisa ga taken taro da matakan da aka tsara da ma tasirinsa kan kasashen na Afirka, taron kolin ya sake nanata sahihancin alakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka da kuma kudurinsu na bai daya kan ci gaban duniya baki daya.

Idan aka kalli nahiyar Afirka a matsayin nahiya mai cikakken fata da tarin albarkatu, kasar Sin na kokarin taimakawa Afirka amfani da hanyoyin da suka dace da yanayinta wajen farfado da kanta. Kasar Sin tana mutunta muradun kasashen Afirka, kuma a sabon zamanin da ake ciki, tana kokarin hade shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar kungiyar tarayyar Afirka game da raya nahiyar nan da shekarar 2063 da kuma matakan raya kasashen nahiyar daban-daban.

Yadda kasar take kokarin taimakawa kasashen Afirka, ya taimakawa baki dayan al'ummomin kasashen biyu da suka tasamma biliyan 2.6 sama da kaso 1 bisa 3 na yawan al'ummar duniya.

Saboda muhimmancin da take baiwa muradun al'ummomin kasashen biyu, kasar Sin tana amfani da ci gaban da ta samu wajen raya kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana taimakawa kasashen Afirka a fannin rage talauci, kara samar da guraben ayyukan yi da kudaden shiga da inganta rayuwar al'umma.

Don haka wannan ya rage ga mazauna Sin da Afirka su auna yanayi da tasirin alakar sassan biyu. Misali rahoton da shugaba kasar Djibouti Isma'il Omar Guelleh ya gabatar, yana mai cewa, kaso 89 cikin 100 na 'yan Afirka ne ke aiki a kamfanonin kasar Sin dake aiki a Afirka abin da ke nuna cewa, an samar da miliyoyin guraben ayyukan yi a sassa daban-daban na nahiyar.

Yayin da take gudanar da hulda da kasashen Afirka, har kullum kasar Sin tana nuna hali da gudanar da abubuwa yadda ya kamata.

Karkashin alakar sassan biyu, kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa kasashen Afirka a fannin samar da abinci nan da shekarar 2030, da kara bude hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Sin da kasashen Afirka, da fadada musaya da hadin gwiwa wajen magance matsalar sauyin yanayi, da kafa asusun tabbatar da zaman lafiya da tsaro na Sin da Afirka. Sauran fannonin sun hada da samar da taimako ga matasa da harkokin kiwon lafiya da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu da wasu sauran matakai.

Sabbin matakan hadin gwiwa guda 8 da mahukuntan kasar Sin suka gabatar, sun mayar da hankali ne kan abubuwan dake kawo cikas ga ci gaban Afirka. Don ganin an cimma wadannan manufofi, kasar Sin ta yi alkawarin wani sabon shirin tallafin kudi na dala biliyan 60.

A jawabinsa shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta kudu, ya ce alakar Sin da Afirka, za ta taimaka wajen kara karfin Afirka tare da samar da sabbin masana'antu.

Shi kuma shugaba Paul Kagame na Rwanda, ya yi watsi da yadda wasu ke yiwa alkarar Sin da Afirka bahaguwar fahimta, yana mai cewa, dukkan bangarorin na amfana da wannan alaka, kuma duk wanda ke gudanar da harkokin kasuwanci a nahiyar shi ma yana cin gajiyar wannan dangantaka.

A yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gayyaci kasashen Afirka da su shiga jirgin raya kasar Sin a jawabin da ya gabatar, yadda baki daya kasashen Afirka da suka hallara a babban dakin taron jama'a suka jinjina masa ya nuna cewa, matakan kasar Sin sun dace da abubuwan da take gudanarwa game da Afirka.

Hadin gwiwar Sin da Afirka ta kara bunkasa alakar kasashen masu tasowa da kara himmatuwa wajen inganta tsarin tafiyar da harkokin duniya. Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ke cewa ne, taron kolin FOCAC na Beijing, ya nunawa duniya karara cewa wajibi ne, nan gaba duniya za ta karkata ga akalar moriyar juna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China