in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin FOCAC ya samar da kuzari ga ci gaban kasashen Afirka ta wasu fannoni uku
2018-09-06 21:31:48 cri

Kwanan nan aka kammala taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a nan birnin Beijing. Taron dai ya zartas da sanarwar Beijing, da kuma shirin matakan da za a dauka nan da shekaru uku masu zuwa, wadanda suka jawo hankalin Sin da kasashen Afirka, har ma da na duniya baki daya. A ganin shugabannin kasashen Afirka mahalarta taron, "Sin aminiya ce da Afirka ke iya dogara a kai", musamman ma sabbin manufofi da matakai da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da kara tabbatar da kyakkyawar makomar Sin da kasashen Afirka ta bai daya, matakin da zai iya haifar da babban tasiri ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma dauwamammen ci gaba a nahiyar Afirka.

Wadanda suke da ilmi kan tarihin cudanyar al'ummar Sin da kasashen Afirka sun san cewa, gaskiya ce shugabannin kasashen Afirka suka fada a maimakon zancen nuna bakunci. A yayin da Sin ke cudanya da kasashen Afirka, ta fi mai da hankali a kan rikon gaskiya da sahihanci, tare kuma da tabbatar da muradun da ake son cimmawa, da kuma martaba ka'idojin da ya kamata a bi.

Yadda aka mai da muhimmanci a kan daukar matakai, abu ne da ya bambanta hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Afirka da sauran sassan duniya. A gun taron koli na wannan karo, bisa ga shirye-shiryen hadin gwiwa guda goma da aka gabatar, a gun taron kolin dandalin FOCAC da aka gudanar a shekarar 2015, a wannan karo kasar Sin ta kuma gabatar da wasu manyan matakai takwas da za a dauka nan da shekaru uku masu zuwa, wadanda suka shafi bunkasa masana'antu, da ababen more rayuwa, da saukaka harkokin cinikayya da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli, da inganta kwarewar kasashen, da kiwon lafiya, da musayar al'adu da kuma tsaro. Kuma babu shakka, matakan za su samar da kuzari ga bunkasuwar kasashen Afirka ta fannoni uku.

Da farko, hakan na iya biyan bukatun kasashen Afirka, don taimaka musu wajen cimma burin samun ci gaba. A shekarar 2015, aka zartas da ajandar shekarar 2063 a gun taron kolin kungiyar AU, inda aka tsara wa 'yan Afirka wata taswira game da raya "wata nahiyar Afirka da suke so" a fannoni guda 7, ciki har da ci gaban tattalin arziki, da hadin kan siyasa, da zaman lafiya da tsaro, da demokuradiyya da doka, da amincewar al'adu, da mayar da jama'a a gaban komai, da kuma tasiri a duniya da dai sauransu.

Idan ana son cimma wannan buri, abun da ya fi muhimmanci a gaban komai shi ne, a warware matsalolin da nahiyar ke fuskanta, wajen koma bayan manyan kayayyakin more rayuwa, da rashin kwararru da kuma rashin kudi.

Ko manyan shirye-shiryen hadin kai guda 10 a tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka gabatar a shekarar 2015, ko manyan matakai guda 8 da aka gabatar a taron kolin bana, ko kuma shirye-shiryen kudi da ayyuka masu nasaba da hakan, dukkan su matakan hadin kai ne da kasar Sin ta gabatar, game da hadin kai a tsakaninta da Afirka domin biyan bukatun Afirka, kuma suna dacewa da fannonin da ake nuna fiffiko a kai wajen neman ci gaban tattalin arziki da al'ummar Afirka.

Don haka, a yayin da yake zantawa da manema labaru a kwanan baya, babban daraktan sashen kula da harkokin Turai, da gabas ta tsakiya, da kuma Afirka na cibiyar neman ci gaba ta kungiyar OECD Arthur Minsat ya bayyana cewa, shawarar matakai guda 8 za ta yi amfani wajen inganta matsayin masana'antu da na ba da ilmi a nahiyar Afirka, da kuma taimaka wajen tabbatar da ajandar shekarar 2063 ta AU.

Na biyu, zai kara imanin 'yan Afirka kan makomar ci gaban nahiyarsu. Nahiyar Afirka na da dogon tarihi, da yawan albarkatu, amma sakamakon mulkin mallakar yammacin duniya a tarihi, da sabon ra'ayin 'yanci na yammacin duniya a shekaru 80 zuwa 90 na karnin da ya wuce, wasu kasashen Afirka da dama ba su samu 'yanci sosai ba a fannin tattalin arziki, sun kuma fuskanci danniya a fannin siyasa. 'Yan Afirka na fatan cimma burin samun dauwamammen ci gaba bisa karfin kansu, amma ba su san yaya za su cimma burin sosai ba.

Tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000, a cikin shekarun 18 da suka gabata, ba kawai kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka kasuwa, kudi, fasaha ba, har ma ta kawo musu fasahohin neman ci gaba, hakan ya karawa kasashen Afirka imani a neman tsarin ci gaban tattalin arziki da zai dace da yanayinsu. Daraktan sashen kula da harkokin Afirka na OECD Abebe Aemro Selassie yana ganin cewa, nasarorin da Sin ta samu a cikin shekaru 40 da ta yi gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, sun samar da fasahohin da kasashen Afirka ke iya koya, wajen neman ci gaban tattalin arzikinsu.

A yayin taron koli na dandalin tattauna hadin kai da aka kammala ba da dadewa ba a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, nahiyar Afirka na da makoma mai kyau wajen samu ci gaba, kuma nahiyar na cike da buri kan makomar su, wannan ne kwarin gwiwa da ya yi kan jama'ar Afirka, da kuma wadanda ke kulawa da Afirka.

Na uku, matakai takwas za su kara fadakar da duk duniya kan nahiyar Afirka, da baiwa kasashen duniya kwarin-gwiwar su kara zuba jari da yin hadin-gwiwa da Afirka.

A karshen karnin da ya gabata, an taba lakabawa nahiyar Afirka sunan "maraya", wadda ba ta da muhimmancin sosai a duk fadin duniya baki daya. Bayan da aka kafa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a shekara ta 2000, musamman yayin da ake gudanar da taron koli na Beijing na FOCAC a shekara ta 2006, Afirka ta fara jawo hankalin kasa da kasa. Ministan harkokin wajen kasar Birtaniya na wancan lokaci, Mista William Hague ya taba bayyana cewa: "Duba da irin ci gaban dangantakar Sin da Afirka cikin sauri, mun gano cewa akwai daidaito tsakanin cinikayyar Sin da Afirka. Haka kuma mun kara gano cewa, nahiyar Afirka wata babbar kasuwa ce dake kunshe da mutane sama da miliyan dari takwas(yanzu biliyan 1.2)."

A halin yanzu, Afirka ta zama muhimmiyar nahiya da kasashen duniya da dama ke son zurfafa dangantaka da ita, inda aka gudanar da manyan wasu tarukan koli da dama, ciki har da taron kolin Amurka da Afirka, da taron kolin Turai da Afirka, da taron kolin Indiya da Afirka, da taron kasa da kasa kan ci gaban Afirka da aka yi a birnin Tokyo na kasar Japan, abun da ya nuna cewa, akwai kasashen duniya da yawa wadanda ke son karfafa hadin-gwiwa da Afirka a fannonin diflomasiyya da tattalin arziki. A cikin wani rahoton da bankin duniya ya fitar a karshen shekarar bara, dangane da yanayin harkokin kasuwanci na duniya na shekara ta 2018, an nuna cewa kasashen Afirka guda biyu, wato Mauritius da Rwanda, sun kasance cikin jerin kasashe hamsin dake kan gaba a duniya, wadanda ke da yanayi mai kyau wajen yin kasuwanci.

Bugu da kari, bisa wani rahoton da shahararren kamfanin kula da harkokin akanta na duniya wato EY ya fitar a watan Mayun bara, an ce, a shekara ta 2016, gaba daya Afirka ta jawo hankalin kasashen waje, don su zuba jari kai-tsaye a cikin ayyuka 676, kuma yawan kudin da suka zuba cikin Afirka ya karu da kashi 31.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2015. Game da wannan batu, shugaban kungiyar tarayyar Afirka a wannan zagaye, kana shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, cewa ya yi hadin-gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kawo manyan sauye-sauye ga Afirka, wadda kuma ya sauya matsayin Afirka a duk fadin duniya.

Shi ma a nasa bangaren, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi nuni da cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun dauwamammen ci gaba a Afirka, su ne muhimmin tushe ga sha'anin neman shimfida zaman lafiya da bunkasuwa na MDD, kana kuma hadin-gwiwar Sin da Afirka dake samun moriyar juna, na taka rawar a-zo-a-gani ga bunkasuwar nahiyar Afirka. Dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ya bude sabon babi ga hadin-gwiwar bangarorin biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China