in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar manufar da Xi ya gabatar ta nuna tunanin diflomasiyya mai hallayar musamman ta Sin
2018-09-06 10:53:59 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sabuwar manufar da kasarsa za ta aiwatar a kasashen Afirka yayin bikin bude taron kolin dandalin FOCAC na birnin Beijing, inda ya yi cikakken bayani kan matsayin gwamnatin kasar Sin game da harkokin diflomasiyya da take gudanarwa a kasashen Afirka, masana suna ganin cewa, manufar ta nuna tunanin diflomasiyya mai halayyar musamman ta kasar Sin, haka kuma ta shaida cewa, kasar Sin tana dukufa kan hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka domin samun ci gaba tare.

Yayin taron kolin dandalin FOCAC na Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sabuwar manufa a fannoni biyar, na farko, kasar Sin ba za ta kawo cikas ga kokarin da kasashen Afirka suke yi domin samun ci gaba bisa hakikanin yanayin da suke ciki ba, na biyu, ba za ta tsoma baki a cikin harkokin gidan kasashen Afirka ba, na uku, ba za ta yada manufofinta a kasashen Afirka ba, na hudu, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa yayin da take samar wa kasashen Afirka tallafi ba, na biyar, ba za ta nemi samun moriyar siyasa yayin da take zuba jari a kasashen Afirka ba, kan wannan jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Afirka ta Kudu kuma tsohon shugaban sashen kula da harkokin kasashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Songtian yana ganin cewa, manufar nan ta nuna tunanin diflomasiyyar gwamnatin kasar Sin a kasashen Afirka. Yana mai cewa, "Wasu kasashen duniya sun nuna shakku cewa, me ya sa ake samun zumunci mai zurfi tsakanin al'ummun kasashen Afirka da kasar Sin, hakika, hakan ya biyo bayan manufar diflomasiyyar da kasar Sin ke aiwatarwa ne, gwamnatin kasar Sin ta nace ga ka'idoji guda hudu, wato nacewa ga aminci da sahihanci da nunawa juna mutunci, nacewa ga samun moriya tare, nacewa ga dora muhimmanci kan moriyar al'ummun kasa, nacewa ga yin hakuri da juna da kuma bude kofa, duk wadannan ka'idojin hudu sun nuna tunanin diflomasiyya mai halayyar musamman ta kasar Sin, ana iya cewa, ba zai yiyu kasashen yamma sun kai wannan matsayin ba, wato ba zai yiyu kasashen yamma su aiwatar da irin wannan manufa a kasashen Afirka ba."

Shehun malami a kwalejin harkokin wajen kasar Sin kuma daraktan cibiyar nazarin harkokin kasashen Afirka Li Dan ya bayyana cewa, shugaba Xi ya gabatar da sabuwar manufar ce bisa tushen ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana na kasar Sin wato girmama 'yancin cikakken yankin kasa da juna, rashin kai wa juna hari, rashin tsoma baki a cikin harkokin gida na juna, yin zaman daidaito da moriyar juna, yin zaman tare cikin lumana, ya ce, "A cikin wadannan ka'idoji biyar, abu mafi muhimmanci shi ne rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, yanzu mun kara habaka ka'idar nan, har zuwa fannoni biyar, ina ganin cewa, sabuwar manufar za ta ci gaba da yin jagora kan aikin raya huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a sa'i daya kuma, za ta zama ka'ida mafi muhimmanci yayin da ake kafa sabuwar huldar tsakanin kasa da kasa."

Mataimakin shehun malamin sashen nazarin harkokin kasashen yammacin Asiya da Afirka na cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin Wang Hongyi yana ganin cewa, sabuwar manufar za ta taimakawa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin dogon lokaci, yana mai cewa, "Sabuwar manufar tana da ma'ana matuka yayin da ake kokarin gina kyakkyawar makomar al'ummun Sin da Afirka, saboda kasar Sin za ta kara samun aminci da zumunci daga al'ummun kasashen Afirka ta hanyar gudanar da hadin gwiwa."

Shugaba Xi shi ma ya jaddada cewa, babu wanda zai kawo illa ga hadin kan al'ummun Sin da Afrka, babu wanda zai hana ci gaban farfadowar kasashen Sin da Afirka, babu wanda zai musunta sakamakon da aka samu yayin hadin gwiwar Sin da Afirka, babu wanda zai hana kasashen duniya su samar da tallafi ga kasashen Afirka, jakadan Sin dake Afirka ta Kudu Lin Songtian ya bayyana cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta samu ci gaba cikin sauri, kasar Sin ta taka rawar gani kan ci gaban kasashen Afirka, har al'ummun kasashen Afirka sun nuna godiyarsu, amma wasu kasashe, musamman ma kasar Amurka da wasu kasashen yamma suna ta yada jita-jita kan wannan nasara da aka samu, sabuwar manufar diplomasiyyar kasar Sin a kasashen Afrika ta nuna cewa, duk da cewa, an fuskanci wasu matsala, amma tabbas hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka za ta ci gaba yadda ya kamata."

Jakadan ya kara da cewa, manfuar ta sake shaida cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China