Da yake tsokaci dangane da batun kyautata alakar tattalin arziki da karfafa mu'amala tsakanin kasashen biyu, Li ya ce kasar Sin a shirye take ta bayar da duk wani taimako don bunkasa ci gaban Najeriya, ya ce kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wajen raya cigaban bangarorin biyu tare, ya kara karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwa wajen shiga takarar neman ayyuka a Najeriya musamman a fannonin zuba jari da cinikayya, da samar da kayayyaki da kuma aikin gina kayayyakin more rayuwa ta hanyar bin ka'idojin ciniki domin bangarorin biyu su samu kyakkyawan sakamako na cin moriyar juna.
Shugaba Buhari ya taya wa kasar Sin murnar samun nasarar karbar bakuncin taron kolin FOCAC na Beijing kana ya yabawa kasar Sin saboda taimakon da take bayarwa wajen kyautata rayuwar bil adama, da horas da matasa, da taimakon da take baiwa Najeriya wajen zamanantar da aikin gona, da aikin gina kayayyakin more rayuwa. Ya ce Najeriya a shirye take ta kara zurfafa mu'amalar hadin gwiwar tsakaninta da kasar Sin. (Ahmad Fagam)