in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Chadi
2018-09-05 20:33:24 cri

A Larabar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno, wanda ya kasance daya daga shugabannin kasashen Afirka da dama, da suka halarci taron kolin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na bana a nan birnin Beijing.

Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya jaddada cikakkiyar nasarar da aka samu a yayin taron da ya kammala, yana mai godewa shugaba Deby bisa gudummawar sa a wannan fannin.

Shugaba Xi ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Chadi, wajen aiwatar da kudurori daban daban, wadanda suka hada da gina ababen more rayuwa, da habaka harkar samarwa da sarrafa makamashi, tare da taimakawa kasar ta Chadi wajen zamanantar da masana'antun ta.

Har ila yau shugaba Xi ya ce kasar sa na fatan tallafawa Chadi a fannin karfafa kwarewarta, wajen yaki da ta'addanci, da wanzar da zaman lafiya da lumana.

A nasa bangare, Mr. Deby ya mika sakon taya murnar kammala taron na birnin Beijing cikin nasara, yana mai cewa abun burgewa ne ganin yadda shugabannin kasashen Afirka da dama suka halarci taron, suka kuma yi musayar shawarwari, da aiki tare, duka dai da niyyar ganin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya samu ci gaba bisa kyakkyawan yanayi. A cewarsa, hakan ya shaida yadda kasashen Afirka suka amince da shugabancin Xi Jinping da kasar Sin, tana kuma da imani, da kwarin gwiwa game da nasarar kawancen sassan biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China