in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
2018-09-05 20:18:16 cri

Yau Laraba da safe, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari. Yayin zantawar su, Li Keqiang ya ce akwai kyakkyawar makoma game da habaka hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya a fannin tattalin arziki.

Li ya ce, kasar Sin na fatan samar da goyon-baya da taimako ga Najeriya a bangaren neman samun ci gaba, kuma tana fatan karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwar gudanar da ayyukan hadin-gwiwa tare da Najeriya, musamman a fannonin da suka shafi zuba jari da cinikayya, da raya masana'antu, da samar da muhimman ababen more rayuwar jama'a da dai sauransu, ta yadda za'a samu cimma moriyar juna.

A nasa bangaren, Muhammadu Buhari ya ce, yana taya kasar Sin murnar cimma nasarar gudanar da taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Beijing, wanda a cewarsa, ya kirkiro wata kyakkyawar makoma ga hadin-gwiwar Sin da Afirka.

Shugaba Buharin ya kuma godewa kasar Sin, bisa tallafin jin-kai da ta baiwa Najeriya, da matasan kasar da Sin ta horas, da kuma taimakon da kasar Sin ta bayar wajen inganta muhimman ababen more rayuwar al'umma na Najeriya, domin samar da alheri ga jama'ar kasar. Buharin ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da kokari wajen zurfafa hadin-gwiwa da mu'amala da kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China