in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron koli na FOCAC na Beijing
2018-09-05 14:48:55 cri

A jiya Talata ne, aka rufe taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing, inda aka gabatar da sanarwar Beijing da shirin ayyuka na Beijing, wadanda suka shaida daidaiton da Sin da Afirka suka cimma kan manyan batutuwan duniya, tare da yin imani da hada kai tare wajen aiwatar da manyan ayyuka 8 da sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma neman raya makoma ta bai daya tsakanin al'ummomin Sin da Afirka. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, taron kolin ya bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da zama abin misali na hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ne suka shugabanci shawarwari tsakanin shugabannin kasashe da suka halarci taron kolin Beijing na FOCAC da safe da kuma yamma daya bayan daya, inda aka zartas da takardu biyu. Bayan shawarwarin, shugaba Xi Jinping da shugaba Ramaphosa da kuma sabon shugaban dandalin tattaunawar wato shugaban kasar Senegal Macky Sall sun gana da 'yan jarida tare. Xi Jinping ya bayyana cewa, taken taron kolin na wannan karo shi ne "hada kai da samun moriyar juna, da yin kokari tare wajen neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka", an kuma tsara shirye-shiryen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da kuma hadin gwiwarsu waje guda. Ya ce,

"An gabatar da 'sanarwar Beijing ta neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka' a yayin taron, wanda ya shaida daidaiton da Sin da Afirka suka cimma kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna, da nunawa duniya yadda hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ke gudana. Kana an zartas da ayyukan da ake fatan gudanarwa yayin taron FOCAC na Beijing daga shekarar 2019 zuwa 2021, wanda ya tabbatar da manyan ayyuka 8 da za a aiwatar a shekaru 3 masu zuwa, da kuma kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a dukkan fannoni."

Shugabanni ko wakilai na kasashen Afirka 53 ne suka halarci taron koli na Beijing na FOCAC na wannan karo, Sin da kasashen Afirka sun sake haduwa da juna bayan taron koli na Beijing na shekarar 2006 da kuma taron koli na Johannesburg na shekarar 2015. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ana kokarin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a sabon lokaci, kana akwai kyakkyawar makoma a wannan fanni. Kasar Sin tana fatan hada kai tare da kasashen Afirka wajen yin amfani da damar taron koli na Beijing na wannan karo don raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a dukkan fannoni dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon mataki. Xi Jinping ya bayyana cewa,

"Sin da Afirka za su kara yin hadin gwiwa, da kokari tare don samun moriyar juna da bunkasuwa tare. Sin za ta nuna sahihanci da adalci da imani da zumunta ga Afirka da ra'ayin moriya mai dacewa, da haka za ta kai tare da kasashen Afirka wajen kara sada zumunta da yin imani da juna a tsakaninsu, da sa kaimi wajen raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata."

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka za ta taimaka ga samun ci gaba a Afirka, kara imanin jama'ar kasashen Afirka, da kuma kasa da kasa za su taimaka ga samun kyakkyawar makoma ga bunkasuwar Afirka. Kuma hakan zai sa kasashen duniya su kara mai da hankali kan kasashen Afirka, har ma su kara zuba jari da yin hadin gwiwa a Afirka.

Shugaba Ramaphosa da shugaba Sall sun bayyana a cikin jawabansu cewa, tun bayan da aka kafa dandalin FOCAC shekaru 18 da suka gabata, dandalin na FOCAC ya zama muhimmin dandali na kara sa kaimi ga samun ci gaba a tsakanin Sin da Afirka, musamman ga kasashen Afirka. An samu sakamako mai kyau a yayin taron kolin, wanda ya shaida zumunci mai karfi dake tsakanin Afirka da Sin, tare da tsara shirin raya dangantakar dake tsakaninsu. Kasashen Afirka suna fatan hada kai da kasar Sin wajen zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Afirka da Sin, da raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da bullo da sabbin matakan hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin, da kuma neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka. Shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa,

"Mun amince da nuna goyon baya ga shawarar 'ziri daya da hanya daya' da shugaba Xi Jinping ya gabatar don tinkarar kalubalen da muke fuskanta. Muna son amfani da wannan dama don sa kaimi da kyautata fannonin da kasashen Afirka ke bukata. Muna nuna godiya ga shugaba Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin saboda jarin da ta zuba a manyan fannoni a Afirka, ciki har da gina ayyukan more rayuwa, raya masana'antu, inganta tattalin arziki na teku, kimayya da fasaha, kiwon lafiya, bada ilmi, horar da kwararru da sauransu." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China