in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Rasha da Turkiya da Iran za su gana a Geneva kan rikicin Syria
2018-09-05 09:41:39 cri

A mako mai zuwa ne ake sa ran MDD za ta jagoranci wata tattaunawa tsakanin manyan jami'an daga kasashen Rasha da Turkiya da Iran a birnin Geneve, a wani mataki na kawo karshen rikicin kasar Syria.

Manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya shaidawa taron manema labarai cewa, zai tattauna da wakilan kasashen uku game da yadda za a kafa kwamitin da zai kula da batun kundin tsarin mulkin kasar ta Syria, ta yadda za a samar da wani shiri na tabbatar zaman lafiya na zahiri a kasar ta Syria.

Jami'in na MDD ya ce, a ranar 10 da 11 ga watan Satumban da muke ciki ne zai gana da manyan jami'an kasashen Rasha da Turkiya da kuma Iran. Sai kuma a ranar 14 ga wata, inda zai ci gaba da tattaunawa da manyan tawagogi daga kasashe 7 da suka hada da Masar da Faransa da Jamus da Jordan, da Saudiya da Burtnaiya da kuma Amurka.

A cewar De Mistura, shi ma kwamitin sulhun MDD zai shirya tattaunawa game da batun kasar ta Syria a ranar 20 ga watan Satumba idan Allah ya kai mu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China