in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kishiya ba za ta hana hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ba
2018-09-04 20:32:14 cri

Bana ake cika shekaru 18 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC. Sai dai a cikin shekarun 18 da suka wuce, wasu kasashen yammaci, da kafofin yada labarai, sun yi ta shafa wa hadin gwiwar Sin da kasahen Afirka kashin kaji, amma duk da haka, ko kadan Sin da kasashen Afirka ba su tsaya ba, har ma sun yi ta cimma gagaruman nasarori a hadin gwiwarsu. A yayin taron kolin dandalin FOCAC da aka gudanar kwanan nan a nan birnin Beijing, an lura da cewa, wasu kafofin yada labarai, da kwararru na kasashen yamma da suka saba da nuna kyamar hadin gwiwar, sun fara fidda rahotanni da suka dace da hakikanin gaskiya.

Matsalar bashi na daya daga cikin abubuwan da kafofin yada labarai na kasashen yammaci suka nuna shakku a kai, a game da jarin da Sin ke zubawa a kasashen Afirka. A shekarar 2015, shirin nazarin harkokin Sin da Afirka da aka gudanar a jami'ar Johns Hopkins ya yi gargadin cewa, mai yiwuwa ne kasashen Afirka ba za su iya biyan rancen kudin da kasar Sin ta samar musu ba. Sai dai wani rahoton da jami'ar ta fitar a kwanan baya ya yi nuni da cewa, rancen kudin da kasar Sin ta samar, ba shi ne babban dalilin da ya kawo matsalar basussuka ga kasashen Afirka ba. Hukumomin kudi na kasa da kasa da dama ne, a maimakon wani ko wata suke bin kasashen Afirka basussuka.

Baya ga haka, kafofin yada labarai na kasashen yamma ma sun sha fitar da rahotanni dake cewa, wai shirye-shiryen da kasar Sin ke zuba wa jari basu samar da guraben aikin yi a kasashen Afirka ba. A game da wannan, kafar CNN a kwanan nan, ta ruwaito rahoton da cibiyar nazari ta McKinsey ta fitar, wanda ke cewa, kasar Sin ta samar da miliyoyin guraben aikin yi ga kasashen Afirka, kuma kaso biyu daga cikin uku na kamfanonin kasar Sin na samar da horo ga ma'aikatansu na kasashen. Rahoton ya kuma gudanar da bicike a kan kamfanonin kasar Sin sama da dubu da ke kasashen Afirka takwas, kuma sakamakon binciken ya nuna cewa, kaso 89% na ma'aikatan kamfanonin 'yan Afirka ne.

Kwanan baya, an kara gano ra'ayin dake nuna cewa wai "Tsarin kasar Sin bai dace da halin Afirka ba", a sharhin da aka bayar a yanar gizo ta Financial Times ta kasar Burtaniya. Amma, kamfanin watsa labaru na BBC na kasar ya bayyana cewa, akwai wasu muhimman mutane da dama dake goyon bayan "Tsarin kasar Sin" a nahiyar Afirka. Kamfanin BBC ya ruwaito maganar shugaban bankin raya Afirka Akinwumi Adesina na cewa, "Akwai mutane masu yawa dake nuna damuwa kan kasar Sin. A gani na ba haka ba ne, ina ganin kasar Sin abokiya ce ta kasashen Afirka". Kana ya ruwaito maganar kwararre a fannin zuba jari na kasar Ghana Michael Kottoh wanda ke cewa, "Nahiyar Afirka ta samu hakikanan nasarori wajen hadin kai a tsakaninta da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari da kuma hada-hadar kudi, kuma an daddale wasu ayyuka na samun nasarar juna, kuma ba kamar hadin kai da yammacin duniya da muka yi a tarihi ba, aka yi su ne ba tare da kara wasu sharudda ba,."

Maganar Michael Kottoh ta shaida manufar da Sin ke dauka, kan hadin kai a tsakaninta da kasashen Afirka; wato sam ba za ta yi abubuwan da ba su dace ba, ciki har da kaucewa tsoma baki kan yadda kasashen Afirka ke kokarin neman hanyarsu ta samun bunkasuwa. Kuma, ba za ta yi shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba. Kana, ba za ta tilastawa kasashen Afirka amincewa da dukkanin ra'ayoyinta ba, kana kuma, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa kan kasashen ba a yayin da take samar masu da tallafi. Har ila yau, kasar Sin ba za ta nemi samun wata moriyar siyasa ba, yayin da take kokarin zuba jari a kasashen Afirka. Ko da yake akwai yadda ake kallon hadin kai a tsakanin Sin da Afirka daban daban a yammacin duniya, amma kasar Sin na tsayawa kan imani da cewa, "Al'ummar Sin da kasashen Afirka ne suka fi dacewa su yi magana, a game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashensu. Babu wanda ke iya musunta manyan nasarorin da aka samu sakamakon hadin kai a tsakanin bangarorin biyu." Joseph Stiglitz, wanda ya samu kyautar karramawa ta MDD ta Nobel kan tattalin arziki ya nuna cewa, domin kishi ne kasashen yamma sun zargi kokarin da Sin ke yi a nahiyar Afirka.

Ana kira Afirka "Nahiya dake cike da buri". A yayin da nahiyar ta soma kama hanyar neman ci gaba bayan da ta kawar da yake yake, da yunwa, da talauci, da kuma ja da baya, wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama suna dora muhimmanci kwarai kan hadin kai a tsakanin su da kasashen Afirka.

Ban da dandalin FOCAC, da taron kolin Turai da Afirka, an kuma bullo da taron kolin na kasashen Larabawa da Afirka, da taron koli na Amurka ta kudu da Afirka, da taron koli na Amurka da Afirka, da taron kasa da kasa na ci gaban Afirka na Tokyo, da taron koli na hadin kan Turkiyya da Afirka da dai sauransu. Kullum kasar Sin na amincewa da hadin gwiwar da kasashen Afirka ke yi da sauran sassan duniya ta hanyoyi daban daban, tana fatan ganin nahiyar Afirka za ta samu ci gaba, sakamakon hadin kai a tsakaninta da kasa da kasa.

A halin yanzu, kasashen Afirka suna fuskantar manyan kalubaloli guda uku wajen neman ci gaba, wandada suka hada da rashin ingancin ababen more rayuwa, da rashin isassun kudade, da kuma karancin isassun ma'aikata masu kwarewa. Duk wanda ya ba da taimako ga kasashen Afirka wajen warware wadannan matsaloli, zai iya zama ainihin abokin kasashen Afirka.

An gabatar da "manyan shirye-shiryen hadin gwiwa guda goma" a yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, domin biyan bukatun kasashen Afirka na neman bunkasuwa. Sa'an nan, a gun taron kolin na wannan shekara da ake yi a birnin Beijng, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da "manyan matakai guda takwas" da za a aiwatar cikin shekaru uku masu zuwa, domin raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta fannonin raya harkokin masana'antu, da hade ababen more rayuwa da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma inganta tsaro da dai sauransu. Ko shakka babu, wadannan matakai guda takwas, za su ba da gudummawa matuka, wajen raya karfin kasashen Afirka, na neman ci gaba da kansu, yayin da ake raya bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka cikin yanayi mai kyau.

Sabo da haka, gidan talabijin na kasar Afirka ta Kudu, ya fidda sharhi dake nuna cewa, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na tafiya ne tare da hakikanin nasarori.

Yawan al'ummar kasar Sin da kasashen Afirka, ya kai kashi 1 bisa 3 na dukkanin yawan mutanen duniya, don haka illa kasar Sin da kasashen Afirka su tabbatar da ci gaba da zaman lafiya, da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummominsu yadda ya kamata, za a kai ga cimma burin neman dauwamammen ci gaban duniya baki daya.

Don haka, hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zai ba da taimako matuka wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma daga matsayin kasashe masu tasowa cikin harkokin kasa da kasa. Kamar yadda aka bayyana cikin jaridar Vanguard ta Najeriya, kasar Sin tana dukufa wajen kiyaye tsarin kasa da kasa, kuma ba kamar yadda masu mulkin mallaka suka taba yi ba, Sinawa sun bayyana al'ummar kasashen duniya cewa, kyandir ba zai rasa haskensa ta hanyar kunna sauran kyandura ba, sai dai ya kara haske a duniya baki daya. (Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China