in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peng Liyuan ta halarci taron Sin da Afirka game da yaki da cutar AIDS
2018-09-04 19:35:41 cri
Uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta halarci taro tare da matan shugabannin kasashen Afirka 37, game da yaki da yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki, wato AIDS ko Sida, wanda aka gudanar a nan birnin Beijing.

A taron na yau Talata, uwargida Peng, tare da matan shugabannin kasashen Afirkan, sun kaddamar da wani shiri na musamman, domin dakile yaduwar wannan cuta cikin hadin gwiwa.

Madam Peng wadda ta yi bitar aikin ta, a matsayin jakadiyar yaki da cutar tarin fuka, da cuta mai karya garkuwar jiki ta hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce hada karfi da karfe wajen yaki da cutar HIV/AIDS, ya zama wani muhimmin aiki da ya shafi dukkanin sassan duniya. Kaza lika hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afirka a wannan fanni ya haifar da manyan nasarori da ake fata.

Ta ce Sin da kasashen nahiyar Afirka, tare da sauran sassan kasa da kasa masu ruwa da tsaki, za su fara aiwatar da wani shiri na shekaru 3 tun daga shekarar 2019 dake tafe, domin shawo kan yaduwar cutar HIV/AIDS tsakanin matasa, da kuma bunkasa kiwon lafiya a matakin farko.

Yayin taron, babban daraktan hukumar WHO Tedros Ghebreyesus, da daraktan zartaswar hukumar yaki da cutar ta HIV/AIDS na MDD Michel Sidibe, sun jinjinawa kokarin da kasar Sin ke yi da hadin gwiwar kasashen Afirka, a fannin yaki da wannan cuta, suna masu yabawa kwazon uwargida Peng, wajen yayata manufar kariya da kula da mutanen dake dauke da cutar ta AIDS ko Sida.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China