Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa za su shugabanci shawarwari da safe da kuma yamma daya bayan daya, inda shugabannin kasashen Sin da Afirka za su yi musayar ra'ayoyi kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da batutuwan kasa da kasa da na yankuna da suke sa lura. Bugu da kari ana sa ran zartas da Sanarwar Beijing kan neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka da kuma Shirye-shiryen Beijing na FOCAC daga shekarar 2019 zuwa 2021 a yayin taron. (Zainab)