in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta yabawa sabbin manufofin kasar Sin na bunkasa samar da abinci ga Afrika
2018-09-04 10:53:17 cri
Wani jami'in MDD ya yabawa taron kolin Beijing na 2018 na dandalin hadin kan Sin da Afrika (FOCAC) saboda bullo da wasu sabbin tsare tsare da nufin tallafawa sha'anin samar da abinci ga nahiyar Afrika.

Gabriel Rugalema, wakilin hukumar samar da abincin ta MDD (FAO) a kasar Kenya, ya ce sabbin manufofin za su taimaka wajen magance matsalar abinci da kuma habaka aikin gona a kasashen Afrika kuma zai taimakawa kasashen wajen cimma muradunsu na bunkasa masana'antu.

A lokacin taron kolin dandalin na FOCAC kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa Afrika wajen cimma nasarar samar da abinci nan da shekarar 2030, Sin za ta yi aiki tare da Afrika wajen aiwatar da shirin da kuma daga matsayin hadin gwiwar Sin da Afrika game da batun bunkasa noma na zamani.

A yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin a birnin Nairobi, Rugalema ya ce, baya ga samar da wadataccen abinci, sabbin manufofin za su sauya fasalin aikin gona ta yadda zai kasance wata babbar hanyar samar da ayyukan yi, da kuma kawo sauye sauye masu ma'ana ga ci gaban rayuwar al'umma.

Rugalema ya bukaci kasar Sin da ta samar da fasahohin aikin gona wadanda nahiyar Afrika ke bukata wajen bunkasa fannin samar da abinci.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China