in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya shirya liyafa ga shugabannin da suka halarci taron kolin FOCAC na Beijing
2018-09-04 09:32:45 cri

A jiya da yamma ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin da mai dakinsa Madam Peng Liyuan suka shirya wata gagarumar liyafar maraba ga shugabannin kasashe da matansu wadanda suka zo kasar Sin don halartar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka bude a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya ce, a cikin shekaru 12 da suka gabata dangantaka tsakanin Sin da Afirka ta bunkasa sannu a hankali inda sassan biyu suka yi karfafa musaya da zurfafa alaka a dukkan fannoni.

Ya ce, a shirye kasarsa take ta hada kai da kasashen Afirka wajen cika alkawuran da ta yi a zahiri, ta kuma rubuta tarihi a aikace, ta yadda al'ummomin Sin da Afirka za su rayu cikin farin ciki, kana dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka za ta ci gaba da fadada a nan gaba.

A nasa jawabin, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa wanda ya kuma jagoranci kaddamar da taron kolkin da aka bude a jiya Litinin, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin kafa ta alakar kasashe masu tasowa da ma kungiyoyi daban-daban

Ya ce, kasar Sin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa ce wajen cimma nasarar ajandar kungiyar tarayyar Afirka game da raya kasashen nahiyar nan da shekarar 2063. Yana mai cewa, taron kolin zai daga matsayin alakar Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China