in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kuwait ta yi tir da harin da Boko Haram ta kai arewa maso gabashin Nijeriya
2018-09-04 09:25:29 cri
Sarkin Kuwait Sheikh Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, ya yi tir da harin da kungiyar Boko Haram ta kai a arewa maso gabashin Nijeriya.

Kamfanin dillancin labarai na KUNA na kasar, ya ruwaito Sarkin na jajantawa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya na mai kuma bayyana yadda Kuwait ke adawa da duk wani nau'in ta'addanci.

Da yake yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa, Sarki Sabah Al-Ahmad ya ce harin ya sabawa dukkan dokokin jin kai.

Akalla sojojin Nijeriya 30 mayakan Boko Haram suka kashe a wani hari da suka kai wa sansanin sojin dake kusa da iyakar kasar da Niger. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China